Daya daga cikin fitattun jaruman shirin fina finan Hausa a masana'antar Kannywood da ta dade tana taka rawa watau Rukayya Dawayya ta bayyana ainahin musababbin dalilin da yasa auren ta yayi saurin mutuwa tun ba'aje ko ina ba tare ma da wasu matsalolin da ta fuskanta a rayuwar auren na ta.
Jarumar dai ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da majiyar mu ta jaridar Blue Print, inda ta ce ita tayi danasanin auren tsohon Mijin na ta Adamu Teku domin kuwa a cewar ta, bata yi cikakken bincike ba game da shi kafin auren.
;
NAIJ.com dai ta samu cewa auren na Rukayya wadda aka fi sani da Dawayya ya mutu ne shekaru kimanin hudu bayan auren, a lokacin da ta kai ma mahaifiyarta ziyara bayan dawowarta gida Najeriya daga kasar Saudiyya inda ta yi auren.
“Allah na gani na yi iya bakin kokarina don ganin aurena ya zauna lafiya, amma hakan bai yiwu ba, saboda mijina auri saki ne, kafin ni ma ya saki mata sama da 15, don haka ba kai na farau ba. Inji jarumar.
No comments:
Write Comments