An dawo da sandar iko na majalisar dattawa da aka sace a ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu.
Wwasu yan iska da ake zargin suna yiwa Sanata Ovie Omo-agege ne suka sace sandar daga zangon majalisa a ranar Laraban.
A martaninta majalisar dattawan ta ba hukumomin tsaro sa’’o’i 24 domin su nemo sandar wanda aka sace.
A safiyar ranar Alhamis ne hukumar yan sanda ta sanar da cewar anga sandar a karkashin wani gada a Abuja.
bayan sa’o’i kadan bayan wannan sanarwar, yan sanda sun dawo da sandar ga majalisar dokoki.
Da misalin karfe 11:50 na safe, wata mataimakiyar sufeto janar nay an sanda, Habila Joshak ta mika sandar ga magatakardan majalisar, Mohammed Sani-Omolori.
No comments:
Write Comments