Wednesday

Home An yiwa gwamnonin APC zanga-zanga bisa zarginsu da yunkurin cin amanar Buhari
Gungun wasu mambobin APC sun mamaye ofishin APC na kasa domin nuna goyon bayansu ga shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole, shugaban kasa Muhammadu Buhari da jagoran jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu. Masu zanga-zangar, karkashin wata kungiya mai goyon bayan Buhari (FBSG) sun isa shelkwatar jam'iyyar a ayarin motoci. Jagoran masu zanga-zangar, Alhaji Ibrahim Sikiru, ya zargi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na jihar Ekiti, Kayode Fayemi, na Kaduna, Nasir Elrufa'i, na jihar Ogun, Ibikunle Amosun, na jihar Adamawa, Jibrilla Bindow da wasu da dama da yunkurin kulla rikici tsakanin Oshiomhole da kwamitin zartarwa na APC.
                                           arewasound

Sikiru ya bayyana cewar sun shirya zanga-zangar ne domin tona asirin jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC da ke kokarin kawar da Oshiomhole da kassara takarar Buhari ta hanyar jawo masa faduwa zabe a jihohinsu. 
"Yanzu haka idan aka yi zabe, shugaba Buhari ba zai samu koda kashi 10% na kuri'ar mutanen jihar Ondo ba saboda kashe masa kasuwa da gwamna Akeredolu ke yi ta hanyar rashin tabuka komai ga jama'a tun bayan hawansa gwamna bisa tsautsayi. "Mun san cewar yanzu haka shine ke yawo daga arewa zuwa kudu domin tattara sa hannun gwamnonin APC da niyyar tsige Oshiomhole. "Akeredolu bai damu da halin da jam'iyyar APC za ta shiga ba saboda ba za ai zaben gwamna a jihar sa ba a 2019," a cewar Sikiru.
Kazalika ya ce masu son ganin an kawar da Oshiomhole na jin haushin kin karawa ubangidansu, John Oyegun, wa'adi tare da bayyana cewar mambobin jam'iyyar APC na bayan Oshiomhole dari bisa dari.

SOURCE : LEGIT.NG
No comments:
Write Comments