Thursday

Home Bãna Bada Tallafin 10,000 Jama'a Kuyi Hankali Da "yan Damfara : ATIKU
Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nesanta kansa da wasu tsarin tallafi dake yawo a kafafen sadarwar wanda ake cewa shine ya hidimar tallafa ma jama’a da jarin naira dubu goma goma. 

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Atikun ya bayyana haka ta bakin kungiyar yakin neman zabensa, inda cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a garin Abuja ta bayyana cewa babu hannun Atiku ko na kungiyar yakin neman zabensa a cikin wannan lamari. 


Mun samu rahoton wani tsarin tallafi mai taken ‘Atiku Disbursement Program’ dake kira ga jama’a dasu bada wani adadi na kudi, wanda zasu ninka musu a matsayin tallafi ne daga Atiku Abubakar, bamu da hannu a cikin wannan lamari, da ire irensa. “Kuma mun shaida ma jama’a cewa sahihan hanyoyin kafafen sadarwar Atiku Abubakar na zamani sune; www.atiku.org (Blog) 

Atiku


Daga karshe sanarwar ta yi kira ga jama’a dasu yi watsi da duk wata sanarwar da ake ikirari daga ofishin Atiku Abubakar suka fito, matukar ba daga kafafen sadarwar nan na zamani suka fito ba. daga haka kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2019 ta bukaci jama’a da kada su kuskura su fada wannan tarko nay an damfara, yan damfarar dake kokarin sun bata ma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku suna. 

SOURCE : HAUSA.LEGIT.COM
No comments:
Write Comments