Rahoton kamar yadda jaridar Legit.ng ta kalato daga shafin jaridar This Day ya bayyana cewa, uwargidan shugaba Buhari ta yiwa Oshiomhole katanga da shiga harabar gidan su na zama watau makwancinsu dake cikin fadar ta shugaban kasa a babban birnin tarayya.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, uwargidan shugaban kasar ta jaddada cewa muddin Oshiomhole na da bukatar ganawa da Mai gidanta to kuwa ya ja linzamin dokinsa iyaka ofishin sa dake fadar shugaban kasa ba tare da karasowa makwancin su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, Uwargidan shugaban kasar ta fusata akan Oshiomhole dangane da yanayi na jagorancinsa a jam'iyyar APC, inda a halin yanzu tana daya daga wasu makusanta Shugaba Buhari da kuma wasu gwamnoni na jam'iyyar dake kulla tuggu na tumbuke shi daga kujerarsa.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Uwargidan shugaban kasa ta bayar da umarni ga jami'an tsaro akan yiwa tsohon gwamnan na jihar Edo katanga da shigowa harabar gidan su na zama dake cikin fadar shugaban kasa.

Makonni kadan da suka gabata Aisha Buhari ta kausasa harshe dangane da shugabancin jam'iyyar APC ya gudanar da zabukan fidda gwanaye a kasar nan a sakamakon dambarwar da biyo baya, inda ta ce jam'iyyar ta yi yaudari manufa gami da akidarta ta gaskiya da adalci tare da dakile kwararar romon dimokuradiyya.
No comments:
Write Comments