Sunday

Home Rage kudin mai: Atiku ya fito da jahilicin sa a bangaren tattalin arziki a fili. : Ezekwesili
Oby Ezekwesili wanda za tayi takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawar ACPN, tace alkawarin da Atiku Abubakar yayi na karya farashin man fetur idan Jam’iyyar ta ci zabe a 2019 ya nuna cewa bai san abin da yake yi ba.

Atiku Abubakar wanda shi ne ‘Dan takarar PDP yayi alkawarin maida litan man fetur kusan N90 idan ya zama Shugaban kasa wanda Oby Ezekwesili take ganin hakan ya tabbatar da cewa Atiku bai san komai ba game da tattalin arziki.
Mai neman kujerar Shugaban kasar tace alkawarin da PDP take yi na rage kudin man fetur ba komai bane illa 419 domin yaudarar mutanen Najeriya. Ezekwesili tace Gwamnati ba za ta iya rage farashin litan man fetur a Najeriya ba.

Misis Obiageli Ezekwesili tace wannan alkawari ya nuna cewa kasuwancin Atiku na bogi ne ba komai ba. Ezekwesili ta kuma idan ta samu mulki, talaka zai ji dadi domin za ta soke tsarin tallafin man fetur na karya da Gwamnati ta ke biya. Idan ba ku manta ba, a makon da ya wuce ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace tattalin arzikin Najeriya garau yake a halin yanzu inda ya kuma sha alwashin cigaba da bunkasa tattalin kasar a mulkin sa.






Read more: legit hausa.ng
No comments:
Write Comments