Thursday

Home Harin Makiyaya ya salwantar da rayuka 10 a wata jihar Arewa
Cikin duhu a dare Kimanin rayukan mutane 10 sun salwanta a wani sabon hari na makiyaya da ya auku cikin kauyen Tse loreleegeb da ke karkashin karamar hukumar Guma a jihar Benuwe.
Ta'addanci

Shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, hukumar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da salwantar rayukan mutane biyar yayin aukuwar wannan mummuman hari cikin duhu a dare.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan da suka kutso daga makociyar jiha ta Nasawara a daren Talata sun yi aman wuta na harsashin bindiga kan duk wanda suka riska.

Ba ya ga kisan kiyashi da suka yiwa al'umma, maharan sun kuma kone gidaje, bukkoki, da kuma gonaki a yankin na gundumar Babai.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a halin yanzu al'ummar kauyen sun nemi mafaka a kauyuka na kurkusa da ke garin Daudu a sakamakon fargaba ta abinda ka iya biyo baya.

Shugaban karamar hukumar Guma, Mista Anthony Shawon, yayin tabbatar da aukuwar harin da ya salwantar da rayukan mutane goma, ya ce maharan sun kutso daga makociyar jiha da ta kasance Nasarawa.

Ya yi kira ga hukumomi masu ruwa da tsaki kan tabbatar da tsaro a yankin, da su sanya wani shamaki na tsananta bincike akan iyaka ta jihar Benuwe da kuma Nasarawa.

KARANTA KUMA: Yadda Hukumar INEC tayi min kwangen kuri'u a jihohi 31 - Atiku Ya Bayyana sakamakon zabe.

Yayin tabbatar da aukuwar hari tare da kira na tsananta tsaro, Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta ce kawowa yanzu bincike ya tabbatar da salwantar rayukan mutane biyar da suka riga mu gidan gaskiya.

A na sa bangaren, Kwamandan rundunar dakarun soji ma su aikin sintiri a yankunan Arewa ta Tsakiya, Janar Adeyemi Yekini, ya ce tuni bincike ya kan kama domin kwance duk wata tufka da warwara da ke tattare da aukuwar hari.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments