Wasu da ake zargin yan iska ne sun kona wani ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Ibesikpo Asuntan da ke jihar Akwa Ibom.
Lamarin da ya afku ana gobe zaben gwamnoni da na majalisar jihohi yayi sanadiyar lalacewar wasu kayayyakin zabe.
Wani idon shaida ya fada ma jaridar The Cable cewa yan sanda sun yi nasarar kare wasu kayayyakin zabe.
Akwa Ibom na daga cikin jihohin da aka samu yawan rikice-rikice a lokacin zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokokin kasa.
Mike Igini, kwamishinan zabe na jihar, ya ziyarci inda abun ya afku. Sai dai babu wani bayani da ke nuni ga ko lamarin zai shafi zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris a yankin.
A wani lamari na daban, Legit.ng ta raoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a daren jiya, Alhamis, 7 ga watan Maris.

No comments:
Write Comments