Showing posts with label fasaha. Show all posts
Showing posts with label fasaha. Show all posts
Thursday
Open Facebook Account With Invisible Name, Yadda Zaku Bude Fb Account Ba Tare Da Suna Ba.
Barka da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya.
Yau muna tafe da bayani akan yadda zaku bude FACEBOOK ba tare da suna a jiki ba.
Step 1) Da farko ku bude wannan link http://facebook.com a wayoyinku na android, sannan ku danna Create New Account.
Step 2) Sai ku canja yaren English Zuwa Yaren Tamil language. Kamar yadda kuke gani a hoton kasa
To Yanzu sai ka nutsu da kyau,, Sannan kabi wadannan steps a nitse , da kuma screen shots da zaka gani.
1) invisible name fb account text code : wato sunan da zakayi amfani dashi a wajen first name.
---->ゖゖ 💟@() ゖ ✔<----
Yanzu kayi copy na wannan code dake sama wanda yake tsakani Arrows (between arrows-->__<--) Sai kayi paste a wajen first name.
2) Yanzu sai ka saka lambar wayarka a email box. Kayi amfani da lambar da ba'a taba bude fb account da ita ba. Sannan kar kayi amfani da email, lambar wayarka kawai zaka saka a email box.
3) kayi selecting na Gender.
4) ka cike date of birth.
5) ka cike wajen Password { ka zabi secure password. Wanda yake da capital latter, Lambobi hade da special word kamar su @ $ # : ! ?.}
Step 3) Bayan ka gama ciccikewa sai ka danna Sign Up. Duba wannan screen shot !
Bayan ka dannan singup Zasu turoma da Confirmation Code zuwa lamar da ka saka . Sai kayi amfani da code din kayi comfirm na account naka.
BAYAN DUK KAGAMA WANNAN SAI KA MAIDA YAREN YA KOMA ENGLISH.
Ga yadda zakaga sabon account naka wanda ba suna.
Shikenan yanzu ka bude facebook account wanda ba suna a jiki.
Ku cigaba da kasancewa da wannan shafi mai albarka.
Tuesday

Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020
Assalamu'alaikum Barkan mu da yau, Da fatan kowa lafiya.
Ayau muna ɗauke da cikakken bayani aka Yadda ake connecting na xender ta wayar android zuwa computer ta hanyar wifi, wannan hanya tanada mauƙar sauri wajen tura files zuwa kan computer ko kuma turawa daga computer zuwa kan waya, a wannan zamani cigaba yazo matuƙa sakamakon idan kukayi duba zuwa shekarun suka gabata ana amfani da bluetooth ne wajen transper na files daga wannan wayar zuwa wannan wayar, a yanzu kuma cigaba yazo ida ake amfani da Xender wadda tafi bluetooth sauri nesa ba kusa ba, idan kuka biyo wannan rubutu namu a yanzu zaku laƙanci yadda ake connecting na android xender da kowacce irin computer, wannan yana aiki akan kowacce waya matuƙar dai android ce.
Aika files ta amfani da wannan hanyar yana da matuƙar sauki da kuma saurin aiki.
Mene yasa zanyi amafani da wannan hayar don kawai tura files zuwa computer?
- Yana iya kasancewa USB naka ya lalace.
- Wayarka ta android bata iya connecting da computer.
- Kana son Tura Large files kamar Bidiyoyi ko kuma Games masu Nauyi.
- Ko kuma dai kawai kanason gawadawa don Gaba.
Abubuwan da ake buƙata sune :
- - Wayar Android , Application na Xender a cikin wayarku ta Android
- - Computer , Chrome, firefox ko opera ko kuma duk wata browser mai ƙarfi a cikin coputer ku.
Step 1.
Ku buɗe xender Application na cikin wayarku ta Android, sai ku taɓa icon na option wanda yake a sama daga ɓangaren hagu, (duba hoton ƙasa).
Step 2.
Bayan kun taɓa wannan icon na option, Da zarar ya buɗe zakuga inda aka saka Connect to PC, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Step 3.
Bayan kun taɓa Connect to PC , waje na gaba zai buɗe , anan zakuga option guda biyu, akwai WEB CONNECT akwai HOT SPOT, to ku Zabi Hot spot kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa, sai ku taɓa CREATE HOT SPOT , zaku ganshi daga kasa. (duba hoton kasa)
Step 4.
Bayan kun taɓa create hot spot, zai fara loading bazai ɗauki lokaci ba , cikin ƴan sakanni zai nuno muku wasu Lambobi, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Sai ku kwafi Wannan lambobin ku rubutasu dai-dai a address bar na browser ta computer ku, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Kuna dannawa zai fara loading , cikin ƴan sakanni zakuga wayar ku ta android tayi motsi (ba motsin jiki ba), To sai ku taba Accept, kamar haka⤵⤵⤵
Shikenan A yanzu kunyi connect na Android da Computer ta hanyar Amfani da Xender Application, Yanzu mun gama bayani akan yadda ake connect ,sai bayani akan Yadda Zaku tura files tsakanin computer zuwa waya ko daga wayarku zuwa computer, sai ku biyo mu.
YADDA AKE TURA FILES DAGA COMPUTER ZUWA A WAYA TA HANYAR AMFANI DA XENDER.
Bayan kun gama da gabaɗaya waɗancan matakan na sama wato yadda ake connect, bayan komai yayi connected to a lura, za'ayi amfani da computer ne wajen aikin walau tura files zuwa waya ne ne ko kuma tura files daga waya zuwa computer ne , to duka da computer zaku yi, waya kuwa sai dai ku ajiyeta a gefe kuma.
Ku biyo waɗannan matakan don sanin yadda ake turawa.⤵⤵⤵
Step 1.
Bayan komai yayi connected, idan kuka duba screenshoot na ƙasa zakuga inda aka sa UPLOAD MUSIC , to wannan button na upload shine zai baku damar aikawa da files zuwa wayarku ta Android wadda ku ka ajiye a gefe.Step 2.
A wannan hoton na ƙasa kuma zakuga inda aka saka alamar DOWNLOAD, wato daga gefen Upload Button, to wannan Download button shine zai baku damar turo files daga wayarku dake ajiye a gefe zuwa computer.
DUBA WANNAN KUMA.
- Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki
- Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min
- Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.
- Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)
- Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020.
Ko kuma Ku ziyarci Page namu mai tâken YADDA AKE....🔗🔗
Bayani Akan Sabon Starin Startup Nigeria Program 2019 https://t.co/h1MwKnPSwG https://t.co/h1MwKnPSwG June 14, 2019 at 01:21AM— AREWASOUND (@Arewasound) June 14, 2019
Sunday

INEC : YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .
YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .
Yau saura kwanaki 2 kacal wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na kowane mai son yin za6e a 2019 ya garzaya maza6ar da yayi rajista domin tabbatar da sunan sa. Tare kuma da kai korafin sa a cibiyar mazabar sa (ward center) idan bai ga sunan sa ba, ko kuma akwai matsala a sunan na sa.
GA DAMA TA SAMU !
Idan ba ka da iko na zuwa mazabar ka domin duba sunan ka, to za ka iya amfani da wayar ka domin duba sunan ka.Ga yadda abin ya ke :
HANYA TA FARKO
1 - bude manhajar ka ta Opera ko UC Browser sai ka yi bincike ta Google a wannan adireshin :Voters.inecnigeria.org
Akwai bayanan katin zaben ka da za a nemi ka cike a wannan shafi :
i- sunan jihar ka,
ii- sunan mahaifin ka,
iii- sunan ka,
iv- kwanan watan haihuwar ka (date of birth).
MISALI :
i- KANO
ii- MUHAMMAD
iii- IBRAHIM
iv- 01-10-2000.
KO KUMA :
(i) sunan jihar ka,
(ii) sunan ka (First name),
(iii) lambobi biyar NA KARSHEN VIN ( Voter's Identification Number ) da ke a cikin katin zaben ka, (kana kuma iya sa su gabaki daya).
Sannan ka aika.
MISALI :
i - KANO
ii - IBRAHIM
iii- 01234.
HANYA TA BIYU
2 - ka aika da sunan # Jihar ka, da # Sunan ka, da kuma lambobi 5 na kashe a VIN naka dake a cikin katin zaben ka zuwa ga WANNAN LAMBA :20120, ko kuma: 08171646879.
MISALI :
KANO
IBRAHIM
01234
zuwa ga 20120, ko 08171646879.
Allah Ya bada sa'a.
A TUNA CEWA KATIN ZABEN KA SHI NE MAKAMIN KA WAJEN FATATTAKAR DUK SHUGABAN BA YA KYAUTATA MAKA, TARE DA ZABEN WANDA KAKE SO YA SHUGABANCE KA.
Allah Ya yi mana zabi mafi alheri. Ameen.
Saturday

Yadda zaku samu Airtel Recharge card Plus 1GB Data *479#
A gaskiya, na buga lambar kuma na samu sako [sms message] daga Airtel cewa ina da kyautar 1GB Data, kuma yana buƙata in sake cajin wasu adadin don buɗe 250MB na mako.
Maganar Gaskiya, bayanin 1GB ba kyauta ba ne. Wasu daga cikcin mutanen mu suna kasa karantawa da kuma fahimtar sakon da aka aika musu Ta hanyar SMS gare su. amma sai su dinga baza bayanai ba daidai ba. Wannan shine dalilin da ya sa muka rubuta wannan post.
kamfanin Airtel Nigeria subyi amfani da shafinsu na yanar gizo don sanar da tsarin na Airtel Recharge Plus * 479 #. A cikin wannan sakon, zan yi bayanin yadda wannan tsarin yake aiki.
Maganar Gaskiya, bayanin 1GB ba kyauta ba ne. Wasu daga cikcin mutanen mu suna kasa karantawa da kuma fahimtar sakon da aka aika musu Ta hanyar SMS gare su. amma sai su dinga baza bayanai ba daidai ba. Wannan shine dalilin da ya sa muka rubuta wannan post.
kamfanin Airtel Nigeria subyi amfani da shafinsu na yanar gizo don sanar da tsarin na Airtel Recharge Plus * 479 #. A cikin wannan sakon, zan yi bayanin yadda wannan tsarin yake aiki.
Yadda za a Saita Airtel Recharge Plus 1GB Data a layin wayarka na airtel
Airtel Recharge Plus shi ne sabon tsarin Airtel wanda yake ba ka 250MB kowane mako idan ka sake cajin adadin da ka gani a saƙon da aka aika maka bayan ka danna * 479 #.
zaku dinga samu 250MB a kowane mako, Suna nufin kenen 1GB a wata. Ba za ku iya amfani da wannan 1GB a haka ba, dole ne sai kun yi cajin kudi a layin ku. Bayan kunyi
chajin kudin ne zasu baku damar amfani da wannan Data 1GB , Wanda zaku samu 250MB a duk sati [mako].
Domin bude wannan free 1GB data,sai kayi chajin kudi dai-dai da adadin da kuka gani a saƙon da Airtel suka aika muku ta hanyar SMS , bayan danna *479# don buɗe Wannan 250MB a duk mako.
zaku dinga samu 250MB a kowane mako, Suna nufin kenen 1GB a wata. Ba za ku iya amfani da wannan 1GB a haka ba, dole ne sai kun yi cajin kudi a layin ku. Bayan kunyi
chajin kudin ne zasu baku damar amfani da wannan Data 1GB , Wanda zaku samu 250MB a duk sati [mako].
Domin bude wannan free 1GB data,sai kayi chajin kudi dai-dai da adadin da kuka gani a saƙon da Airtel suka aika muku ta hanyar SMS , bayan danna *479# don buɗe Wannan 250MB a duk mako.
Friday

Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki
Me Yasa Whatsapp suke dakatar da Lambarka daga Amfani da Manhajara su ta Whatsapp.?
Whatsapp wani fitaccen Application Ne da yake bawa mutane da mar Aika saƙonni nan take, Miliyoyin Jama'a ne suke Amfani da shi a kulli-yaumin, ana iya amfani da shi ta hanyoyi da yawa kamar, aika saƙo na rubutu , na video, na audio ko na hoto, kai harma ana iya yin kira kai tsaye da manhajar ta whatsapp.
Idan ya kasance kana karya dokoki da ka'idojin whatsapp ko kana in wasu halaye da basu kamata ba to ba shakka zasu iya kulle maka account na dan wani lokaci.
Akwai Dalilan da yasa ake dakatar da mutum daga amfani da whasapp, wanda idan har kuka karya su to kuna iya samun matsala da whatsapp, kuskuren farko da mutane sukeyi shine basa karanta sharuddan kafin su bude account na whatsapp, Na kawo wasu manyan dalilai da zai sa whatsapp suyi banning na lambarku ba tare da bata lokaci ba.
Daga cikin dalilan Akwai:-
Whatsapp wani fitaccen Application Ne da yake bawa mutane da mar Aika saƙonni nan take, Miliyoyin Jama'a ne suke Amfani da shi a kulli-yaumin, ana iya amfani da shi ta hanyoyi da yawa kamar, aika saƙo na rubutu , na video, na audio ko na hoto, kai harma ana iya yin kira kai tsaye da manhajar ta whatsapp.
Idan ya kasance kana karya dokoki da ka'idojin whatsapp ko kana in wasu halaye da basu kamata ba to ba shakka zasu iya kulle maka account na dan wani lokaci.
Akwai Dalilan da yasa ake dakatar da mutum daga amfani da whasapp, wanda idan har kuka karya su to kuna iya samun matsala da whatsapp, kuskuren farko da mutane sukeyi shine basa karanta sharuddan kafin su bude account na whatsapp, Na kawo wasu manyan dalilai da zai sa whatsapp suyi banning na lambarku ba tare da bata lokaci ba.
Daga cikin dalilan Akwai:-
- Sending bulk messages to unlisted contacts
- Sharing website URLs and ad links for multiple times a day
- Creating porn & adult-related groups and broadcasts
- Blocking your WhatsApp number by many people
- By uploading content status which is abusive or it may contain adult things.
Wani lokaci , wasu daga cikin dalilan sukan sanya whatsapp suni banning na account na dan wani lokaci, kamar na tsawon awa-72 ko kwana uku, "Whatsapp sunyi banning na lambata har tsawon awa72 daga baya kuma ta dawo aiki".
Domin ka kaucewa irin wannan dakatarwa da whatsapp sukeyi , ya zama lallai kabi dokokin su, ba tare da karya ka'idojin da suka gindaya b, idon karya wasu kananan dokoki, to whatsapp zasu iya kulle maka account a matsayin gargadi, sannan kuma za'a dawo maka da account din bayan kammala kwanakin da suka tsara.
Yadda za a tsere daga WhatsApp Bannig na har abada.
(Wato permanent Ban)
Ko kana aikata irin wancan kuskuren wanda aka zayyano a sama? to karka damu a yanzu haka zaka samu mafita.
Matakan da zakabi wajen dawo da lambarka da aka dakatar daga yin whatsapp.
- Uninstall your existing WhatsApp now
- Download and install new update Whatsapp
- Enter your phone number and you will see a screenshot like this
- - Click on the “Support” option
- - Now a contact support form is displayed like this
- - Write your problem and add the screenshot of what it is showing
- - Don’t forget to add your number
- - Click “Next” and scroll down
- - Choose “This does not answer my problem”
- - Now send a support email using support@whatsapp.com
- - After 4hrs, check your email inbox. You will get a WhatsApp reply.
Ina tabbatar maka ida kabi wannan matakan na sama to lambar ka zata dawo yin aiki a whatsapp.
NOTE ; Idan kuka gwada wannan steps bai yi ba to ku samu wata lambar ku bude sabon whatsapp. abin da ba'a gane ba contact me here, WhatsApp only +2349037621927.

Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole)
Masu binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukar hoton ramin zurmiya na black hole....
A karon farko, masana binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukra hoton ramin zurmina na duniya, abinda ake kira black hole a turance. Shi da ramin black hole shine ginshikin duk duniyoyi da ake iya gani a sararin samaniya kamar yadda bincike ya nuna.
Masanan sunyi amfanin da na’urar Event Horizon Telescope (EHT), wadda ke amfani da jeri-jerin maduban hangen nesa, wato telescopes, da aka giggirka su a kusurwowi daban daban na duniya don leqen abubuwan dake wakana a sararin samaniya.
Hoton ramin, an dauke shi ne a ma’unin M87, wanda yazo daidai da tafiyar shekaru miliyan 55 a kirgar duniyar taurari.
“Wannan hoton da kake gani, yana nuna mana inda ba wani mahaluki da ya taba gani kafin yau” inji Dr Heino Falcke, wani jami’n biciken sararin samaniya na EHT, a lokacin ganawa da maneman labarai, yau a Brussels. Ya kara da cewa “Ni a ganina na, tamkar ace mun dan leko kofar wuta ne”.
DUBA WANNAN : Lauyoyi 12 Ne Za Su Nemawa Amina Amal Hakkinta.
HOTUNA
Dan zobe-zoben dake kewaye da hoton wannan rami dai yazo daidai da hasashen da masanin kimiyyar makamashi, wato Albert Eeinstein ya yi don kwatanta karfin maganadison dake riqe da duniya, wato gravity.
Wannan hoto dai shine sheda mafi inganci dake tabbatar da samuwar ramin zurmiya na black hole da nau’rar Event Horizon ta hasko.
Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole) https://t.co/heoUKnMz1g https://t.co/heoUKnMz1g April 12, 2019 at 02:51PM— AREWASOUND (@Arewasound) April 12, 2019
Subscribe to:
Posts (Atom)















