Showing posts with label labaran ketare. Show all posts
Showing posts with label labaran ketare. Show all posts

Sunday

Amurka ta kai wa Iran hari, ta lalata musu makaman yaki

Wasu rahotanni daga Amurka sun bayyana cewa kasar ta kai wani hari ta yanar gizo (internet) a kan kwamfutocin da dakarun soji na juyin-juya hali a kasar Iran ke amfani da su wajen sarrafa manyan makaman yaki da suka hada da makamai masu linzami (nukiliya).

Rahotanninsun bayyana cewa an ai harin ne a ranar Alhamis bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya canja ra'ayinsa a kan kai hare-hare a wasu wurare mallakin kasar Iran.

Harin da Amurkan ta kai ba zai rasa nasaba da harbo wani jirgin yakin kasar Amurka mai amfani da na'ura da kasar Iran ta yi ba a cikin makon jiya da kuma wani harin da aka kai wa jiragen dakon danyen man fetur na Amurka, wanda ta dora alhakin kai harin a kan kasar Iran.

Babu wata kafar watsa labarai wacce ba ta Amurka ba da ta bayar da tabbacin cewa harin ya lalata makaman yakin kasar Ira.
Shugaba Trump dai ya bayyana cewa kasar Iran ta tafka babban kuskure da ta harbo jirgin yakin kasar Amurka da ake sarrafa wa da na'ura.

Jirgin, maras matuki, da Iran ta harbo na daga cikin jiragen yaki masu matukar tsada da kasar Amurka ta mallaka.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sanda suka yi wa wasu masu garkuwa da mutane dirar mikiya a mafakarsu. 🔗

Trump ya bayyana cewa zai shafe kasar Iran daga doron kasa idan yaki za su yi.
Wutar yaki da ke ruruwa tsakanin kasashen biyu ta jawo zaman dar-dar a kasashen yankin Persia.

Tuni Andrew Murrison, sakataren harkokin kasashen waje na kasar Birtaniya ya isa kasar Iran domin tatauna wa da shugabannin kasar domin yi musu sulhu da kasar Amurka.

Shugaba Trump ya bayyana cewar a shirue yake ya yi sulhu da kasar Iran tare da bayyana cewar kasar Amurka a shirye take idan kasar Iran yaki take so su gwabza. Sai dai, ya gargadi kasar Iran da ta sani cewa Amurka ba tsarar ta ba ce.

POSTED BY LEGIT.NG

DUBA WANNAN KUMA.

- Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

- Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min

- Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.

- Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)  

- Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020. 

Ko kuma Ku ziyarci Page namu mai tâken YADDA AKE....🔗🔗

Thursday

Rikici : Iran ta tarwatsa Jirgin leƙen Asiri na Amurka.

Da safiyar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2019 Kasar Iran ta baro jirgin leken asirin kasar Amurka yayinda rikici ke cigaba da kunno kai tsakanin manyan kasashen guda biyu.



Yayinda jami'an tsaron kasar Iran na ikirarin cewa jirgin Amurkan ta shiga huruminta shi yasa suka barota, amma jami'an Amurka sun ce ba haka bane, jirgi bata shiga hurumin Iran ba a lokacin.
Har yanzu ba'a menene gaskiya lamarin ba.

KU KARANTA: Daga karshe : An Yanke shawarar korar Abdul-aziz Yari daga Jam'iyyar APC. 

Shafin labaran jihar Hormozgan tace:
"Mun baro jirgin leken asirin kasar Amurka. Mun barota ne lokacin da ta shigo hurumin kasar Iran kusa da Koumobarak."

Wannan abu da ya faru shine fito-na-fito na farko tsakanin Iran da Amurka yayinda aka fara cacan baki tsakanin kasashen guda biyu tun hawan mulki shugaba Donald Trump da sanyawa Iran takunkumi.
Amma kasar Amurka ta karyata rahoton Iran cewa an shiga huruminta.


Daya daga cikin abubuwan da sojojin Amurka suka gano a yankin.

Kakakin hukumar sojin Amurka, Bill Urban, yace : "Babu wani jirgin leken asirin da ya shiga hurumin Iran."

Kwamandan hukumar tsaron Iran ya ce wannan abu da kasar tayi sako ne ga kasar Amurka.

Janar Hossein Salami yace Iran ba tasa wani niyyar yaki da wani kasa amma fa shirye take da gwabzawa da kowa.


Monday

Yadda Mohammed Morsi ya yanke jiki ya fadi matacce a kotu

Tsohon shugaban kasar Misra (Egypt), Mohammed Morsi, da sojoji suka yi wa juyin mulki a shekarar 2013, ya mutu a kotu, kamar yadda gidan Talabijin na kasar ya rawaito.

Sashen Turanci na jaridar BBC ya rawaito cewar Morsi ya suma a cikin kotu inda ake tuhumarsa da aikata laifin satar muhimman bayanan sirri (Espionage). Shekarunsa na haihuwa 67.

An hambarar da gwamnatin Morsi bayan shekara daya da hawansa mulki biyo bayan wata zanga-zanga mai zafi.

Tun bayan lokacin yake tsare a kotu.
Morsi ne zababben shugaban kasar Misra na farko, ya hau mulki ne bayan an tursasa tsohon shugaban kasar, Hosni Mobarak, yin murabus.

Bayan an tunkude Morsi daga kan mulki, hukumomin kasar Misra sun shiga farautar magoya bayansa da 'yan kungiyarsa ta 'yan uwa Musulmi (Muslim Brotherhood).

Friday

Ga irin ta nan: Kasar Amurka ta jefa Saudiyya cikin tsaka mai wuya

Dan majalisar wakilan kasar Amurka na babbar jam'iyya mai mulki ta Democrats, Ted Lieu ya gabatar da wani kuduri a gaban majalisar wakilan don neman kawo hanyar da za a kawo karshen sayarwa da kasar Saudiyya makamai daga kasar Amurka.

Sanarwar ta fito daga ofishin kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar, wanda dan majalisar birnin California Ted Lieu ya gabatar da kudurin a gaban shugaban kasar Donald Trump domin ya dakatar da saida wa kasar Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf makamai.

KU KARANTA: Bayani Akan Sabon Tsarin Startup Nigeria Program 2019.  

Sanarwar da dan majalisa Lieu ya gabatar ta ce, a dokar sayar da makamai na kasar Amurka ana duba amfanin da kasar da za a sayarwa makamin zai yi mata, sannan kuma sai an nemi amincewar majalisar dokokin kasar, amma kuma gwamnatin Trump ba ta amfani da wannan dokar kawai sai ta ke yin gamon kanta.

'Yan majalisar wakilai na babbar jam'iyyar Democrats mai mulki Abigail Spanberger, Tom Malinowski da David Cicilline sun gabatar da kudurin sayar da makamai masu linzami a ake iya sarrafasu daga nesa.

Ranar 24 ga watan Mayu ne shugaban kasa Donald Trump ya amince da a sayarwa kasar Saudiyya da wasu manyan kasashe na yankin gabas ta tsakiya makamai ta hanyar amfani da dokar neman amincewar majalisar kasa.Saboda haka ne yasa Trump ba zai nemi amincewar majalisar kasar Amurka ba, inda Amurka za ta sayar da makamai na dala biliyan 8 da miliyan 22 ga kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kasar Amurka dai tayi kaurin suna wurin sayar da makamai ga kasashen duniya, musamman kasashen da suke fama da barazanar yaki da kuma kasashen da suke fama da 'yan ta'adda.

Kasashen da suke sayen makaman sun hada da kasar Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da masu manyan kasashen Gabas ta tsakiya.

Haka a yankin nahiyar Afirka kasar Najeriya ta yi kaurin suna wurin sayen makamai daga wurin kasar ta Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa kasar Amurkan ta bayyana cewa har yanzu babu zancen sulhu tsakaninta da kasar Iran.

SOURCE LEGIT.NG

Wednesday

Kotu ta yankewa malamin Shi'a hukuncin dauri na shekaru 2 a gidan yari.

Wani malamin akidar Shi'a kuma haifaffen kasar Iran ya yankar wa kansa tikitin zama a gidan Dan Kande yayin da wata kotun kasar Faransa ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru biyu bayan sabawa hukumar shige da fice.

Kotun kasar Faransa ta yanke wa malam Muhammad Baraeikechi Ghaleshi hukuncin zaman gidan sarka na tsawon shekaru biyu bayan ta same shi da laifin taimakawaa 'yan ci-rani ketarewa zuwa kasar Ingila ta hanyar kananan jiragen ruwa.

Kazalika kotun ta yankewa wani abokin tarayyar malamin da su ke aikata wannan mummunan harka hukuncin dauri na zama a gidan kaso duk da cewar wa'adin bai kai wanda malamin zai shafe ba wajen bai wa duga-dugan sa hutu.

Bayan gudanar da bincike da sanya idanun lura kan malam Ghaleshi na tsawon watanni kimanin hudu, hukumomin tsaro sun damke shi tare da abokin huldar sa ta aikata wannan babban laifi mai yiwa kowace kasa zagon kasa.

KARANTA KUMA: Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Malama 

Malam Ghaleshi mai shekaru 39 a duniyar kuma malamin akidar Shi'a a birnin Rouen na kasar Faransa ya shiga hannu tare da abokin huldar sa a watan Afrilun da ya gabata bayan kama su da laifin taimakawa 'yan ci-rani masu fafutikar ketarewa zuwa kasar Ingila daga Faransa.

SOURCE LEGIT.NG

An Haramta Jigila Da Jirage Kirar Boeing 737 MAX A Nijeriya Bayan Hatsarin Jirgin Kasar Habasha

Hukumomin Nijeriya sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen haramta jigila da jigragen sama kirar Boeing 737 Max, hukumomin Nijeriyan sun yi hakan ne don tsare rayuka da dukiyar al’ummar kasar,
Air crashes in ethopia, air accident in ethopia.

ministan sufurin saman Nijeriya Sanata Hadi Sirika ne ya bayyana hakan, bayan kammala taron majalisar ministoci da ake duk mako.

Haramcin zai ci gaba har sai an kammala binciken hatsarin jirgin sama kasar Habasha da ya yi hatsari a karshen makon da ya gabata, jirgin Habashan kirar Boeing 737 Max, duk babu wani kamfanin jirgin sama da yake amfani da wannan kirar jirgin, amma hukumomin sun haramta kirar jirgin ma wucewa ta sararrin samaniyyar Nijeriya gaba daya.

‘Hukumar da take kula da jiragen fasinja ta Nijeriya, ita ma ta fitar da takardar haramci ga dukkan kamfanonin jigilar jiragen sama, inda ta bayyana cewa kada wani kamfani ya yi amfani da jirgin wajen sauka ko tashi a dukkan filayen jirgin da ke a fadin kasar nan.’ Inji Sirika

Thursday

'Dan majalissa a Turai ya rasa kujerarsa dalilin satar Burodi.

Mun samu labari cewa wani ‘dan majalisa a kasar Sulobania da ke cikin tsakiyar Nahiyar Turai, ya sauka daga kan kujerar sa, a dalilin satar burodi da yayi a wani shago lokacin da ya je cefane. Gidan jaridar BBC ta rahoto wannan labari.

Darij Krajcic ya rasa kujerar sa ne bayan ya dauki burodi a wani shago a cikin Garin Ljubljana watau babban birnin kasar Sulobania. Wannan ‘dan majalisa yace masu tsaron shagon sun ki kula sa ne lokacin da yake so ya biya kudin
Wannan ‘Dan majalisa, ya fadawa ‘yan jarida cewa ya dauko burodin nan na kwalama mai dauke da ganye da nama watau Sandwich, sai kuma ya iske ma’aikatan shagon su na yi masa yanga a sa’ilin da ya zo da nufin ya sallame su.

Mista Darij Krajcic dai ya faki idanun jama’a ya tsere daga shagon ba tare da biyan kudin wannan burodi ba. Sai dai daga baya ne ‘dan majalisar ya dawo da kan sa domin ya biya kayan da ya dauka yana mai bada hakuri cewa a yafe masa.

Babban ‘dan majalisar mai shekaru 54 a Duniya yace ya aikata hakan ne bayan ya bata lokaci ba tare da an mika masa na’urar POS na biyan kudi ba. Wannan ne fa ya sa jam’iyyun adawa su ka huro masa wuta inda shi kuma yayi murabus.

Wannan abu dai ya ba jama’a dariya, amma shi kuwa ‘dan majalisar na jam’iyya mai mulki a kasar Sulobaniya bai dauki lamarin da wasa ba. Krajcic yace ba a san ‘yan jam’iyyar sa da irin wannan abin kunya ba, don haka ya ajiye aiki.

Wednesday

Wani Likita Ya Kashe Mai Jego Da Jaririnta : Bayan Yasha Ya Bugu.

An kama wani likita a garin Gujarat bisa zarginsa da yin tiyata a yayin da yake cikin mayen giya wadda hakan ya yi sanadiyar mutuwar jariri da mahaifiyarta a ranar Talata kamar yadda 'yan sanda suka sanar.



A cewar yan sandan, an kai mai nakudar, Kaminiben Chanchiya asibitin Sonawala a daren Litinin tana cikin nakuda yayin da likitan Dr. P.J Lakhani ya yi mata tiyata.

Jaririyar mace da aka haifa ta mutu sannan daga bisani Chanchiya itama da mutu wadda hakan ya sanya 'yan uwanta suka zargi likitan da sakaci, inji sufuritandan 'yan sanda, Harshad Mehta.

"Yan sandan sun gano cewa likitan yana buge da giya ne lokacin da ya k bakin aiki a ranar. 

Tuni aka kama shi kuma aka dauki jininsa domin aikewa dashi wajen gwaji," inji Mehta.
Asibitin dai ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan dalilan mutuwar mai jegon da kuma dan na ta domin ganin idan mutuwarta yana da alaka da sakacin aiki ne ko kuma wasu dalilan daban ne suka yi sanadin mutuwar.

'Yan sanda sun shaidawa BBC cewa likitan mai shekaru 50 ne ya kira 'yan sanda da kansa ya nemi su taimake shi saboda yana tsoron iyalan marigayiyar suna iya kai masa hari idan suka gano cewa a buge ya yiwa 'yar uwarsu tiyata.
Wani abu mai kama da wannan ya taba faruwa a garin Ahmedabad a jihar Gujarat inda wanda yarinyar mai shekaru 2 ta rasu yayin da likita ke kula da ita alhalin yana buge da giya.

Likitan mai suna Jayant Patel ya yi ikirarin cewa rashin lafiyar yarinyar ya tsananta ne yayin da ake yi mata magana saboda haka mutuwarta ba shi da alaka da shan giyarsa kamar yadda Times Now ta ruwaito.

Thursday

An Gãno Cewa kungiyar Osama bin Laden ce ta baiwa Boko Haram Makudan kudi har $250,000

A wani littafi da shugaban Boko Haram bangaren ISWA, wanda suke kira Albarnawy, dan gidan Muhammad Yusuf, ya rubuta da Larabci, wanda muka samu fassararsa da turanci, mun tsakuro muku kadan daga cikin irin yadda Boko Haram ke aikinta na kisan gilla da cin zali. A littafin, Albarnawy, ya zayyana yadda bayan kashe mahaifinsa, suka shiga rudani, inda daga baya kwamandojin da mahaifinsa ya baiwa tutar jihadi, suka nada Abubakar Shekau a matsayin khalifansu, a kokarinsu na yin kamanceceniya da yadda Sayyadi Abubakar wai ya gaji annabi bayan wafatinsa.


Boko Haram, wadda ita ma take kokarin sai ta kafa daular Islama a Najeriya, ta bige da kashe mutane ciki har da musulmai, karkashin mulkin Abubakar Shekau, wanda wai ashe cewa yayi tunda Allah ma ya halakar da garuruwan da ake kafirci gaba dayansu, kamar su mutanen Ludu, Adawa da Samudawa, to kuwa wai ya halasta a kone gari baki daya koda da mata da yara, inda a littafin har aka yanko batun Shekau yana cewa: "Ko sanda aka kifar da garin Adawa zaku ce min babu mata da yara da tsofi? Ku kashe! In anje lahira ni Allah zai tambaya!

Subscribe to AREWA24.COM.NG by Email
Su
 dai mabiya da suka ga abin yayi yawa, sun koma kai karar Shekau wurin alqaida wadda ke aiki a yanki Sahara, inda suka je karbar kudi a 2009, har Yuro 200,00, bayan shalkwatar kungiyar ta duniya ta bi diddigi kan irin aikin nasu, da kisan mutanensu da gwamnati tayi, amma tace agaji ne kar su fara yaki da gwamnati sai an shirya, Sai an aiko musu mujahidai zuwa cikin Najeriyar, amma ita kuwa Boko Haram tayi gaban kanta ta fara. 

A littafin, Albarnnawi ya kuma ce sun karbi makamai daga Alkaida a Mali wadanda ita kuma ta samo su daga Mauritania, bayan wani hari da takai na samame cikin kasar, sannan wasunsu sun sami training a Somalia da Mali.

A cikin wasikun da suka yi ta musaya dai, kafin, da bayan sun kwaci garuruwa a yankin arewa maso gabas, daga 2012 zuwa 2014, sun bayyana yadda Shekau ya koma kashe kwamandojinsa da yake zargi da hana shi 'ghanima', ko kuma in yaga sun fara yin karfi.

Albarnawy dai, ya rubuta wa Al-Baghdadi takarda, inda ya tona irin ta'asar da suka tafka karkashin Shekau, bayan ISIL din sun kafa tasu daular a Siriya, ita kuwa ISIL ta sauke Shekau bayan da yayi mata mubayi'a, ta dora bangaren albarnawy, wanda shi kuma shekau yace sai ya halaka su don sunyi ridda suma. A karshe, bangaren Albarnawy, sun aika takardar tambaya kan wai ya halasta su kashe yara a makarantu, da kuma kama yaran mutane mata don bautarwa, da ma wai ko ya halasta su kashe wanda yace duniya a dunkule take? Amsar da suka samu, wadda wani Al-Tamimi ya bayar, jim kadan kafin harin Amurka ya hallaka shi, ya tabbatar musu cewa zasu iya kashe yara a makarantar da soji suka sanya kusa da bariki, ya kuma ce musu bautar wa zasu iya yi, amma banda yaran musulmi, sai dai na Kirista, kuma bai halasta su kashe mutane a masallatai ba, sai dai coci.

Al-Tamimi, ya kuma rufe da basu fatawar cewa ai duniya an riga an gane cewa a dunkule take ashe, don haka su bar kashe mutane don sun ce hakan, su maida hankali wajen kashe soja, da masu bin wasu addinan. Yanzu dai, Boko Haram mai suna ISWA, ta Albarnawy, da wannan manjaha take aiki, a yankin arewacin Borno da tafkin Chadi, su kuma su Shekau suna Sambisa da Sauran kudancin Borno. Kungiyoyin ISIS da Boko Haram dai, duk duniya ta tabbatar kungiyoyin ta'addanci ne marasa tausayi, masu kokarin sai sun zub da jinanen mutane.

Subscribe to AREWA24.COM.NG by Email

Saturday

videon :- guguwar Maria da aka dauka daga tashar 'yan sama jannnati da ke duniyar wata.

Bidiyon guguwar Maria da aka dauka daga tashar 'yan sama jannnati da ke duniyar wata.

Bidiyon guguwar Maria da aka dauka daga tashar 'yan sama jannnati da ke duniyar wata.

Bidiyon guguwar Maria da aka dauka daga tashar 'yan sama jannnati da ke duniyar wata.

ga videon nan kasa.

Download video now

{trt.net.tr hausa}

Koriya ta Arewa ta sake barazanar za ta gwada harba bam din Hydrogen


Alakar Koriya ta Arewa da Amurka na ci gaba da lalace wa inda bayan kalaman da Trump ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Koriyan sake barazanar gwada harba bam din Hydrogen mai hatsari.

A yayin atron Majalisar Dinkin Duniya ne Trump ya ce, idan ta kama su shafe Koriya ta Arewa daga ban kasa to za su yi hakan.
Koriyan dai ba ta yi sanya ba wajen mayar da martani inda ministan harkokin wajenta ya ce, idan fa ba a kyale su ba to za su sake gwada harba bam din Hydrogen wanda babu irinsa a duniya.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce, za su iya daukar kowanne irin mataki don magance Amurka.

{trt.net.tr hausa}

Hhhh hh:-Trump ya mayar da martini kan kalaman Kim Jum-Un.

A cewar shugaban na Amurka, takwaransa na Korea ta arewa Kim Jung-Un baya damuwa da halin da al'ummar kasarsa ke ciki.

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-Un da cewa zai yi nadamar da bai taba yi ba kan zafafan kalaman daya jefe shi da su. Gargadin shugaban Amurkan na matsayin martini ga kalaman da shi Kin Jong-Un ya yi na bayyana Trump a matsayin mai fama da tabin hankali.

A martinin na Trump wanda shi ma ya bayyana Kim Jong-Un a matsayin mai tabin kwakwalwa ya ce tabbas zai dandana kudarsa kuma zai yi nadamar da bai taba yi bat un bayan fara takaddama tsakaninsu.

Da safiyar yau ne dai Kim Jong-Un ya ce akwai bukatar a duba lafiyar shugaban na Amurka Donald Trump bisa ga kalaman da yayi yayin jawabinsa a zauren majalisar dinkin duniya, baya da ya yi alkawarin murkushe kasar ta Korea ta Arewa.

A cewar shugaba Kim, Trump ya muzanta shi ya kuma muzanta kasar sa a idon duniya, yana mai cewa tabbas Trump zai ji a jikinsa inda ya bayyana kalaman na shi a matsayin haushin kare.

Sai dai kuma a martinin na Trump ya ce babu shakka ya tabbata Kim din na da tabin hankali ganin yadda bai damu da halin yunwa da talaucin da al’ummar kasar sa ke ciki ba.

(rfi muryar duniya)

Wednesday

Muhimman Jawabai 5 Na shugaba Muhd Buhari A Taron Majalissar Dinkin Duniya.

Jawabin shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya.

Jawabin shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabai a madadin Kasar najeriya baki daya a taron majalisar dinkin duniya,

1. Batun Nukiliyar kasar Iran, Yarjejeniya akan sauye sauye yanayi na na Farisa da hatsaniyar nukiliyar kasar Koriya ta Arewa

2. Yabawa majalisar dinkin duniya akan rawar da ta taka wajen bayar da matsugunni ga 'yan gudun hijira da yakin kasar Siriya, Iraq da Afgahanistan ya yi ma su sanadiyar zamantakewar su da muhallansu.


3. Godiya ga gwamnatin Jamhuriyyar kasar Jamus karkashin jagorancin Angela Merkel da kuma gwamnatocin kasar Italiya, Girka, Turkey wajen taimakawa dubunnan 'yan gudun hijira.

4. Ya jinjinawa kasashen duniya da al'ummominsu wajen jajintawa, taimakawa da goyon bayan nahiyyar mu da al'ummominmu da yankin tafkin Chadi akan barazanar ta'addancin Al Qa'ida da Boko Haram.

5. Jajintawa da nuna damuwarsa akan rashin kare 'yancin ɗan adam rikicin Gabas ta tsakiya, da kuma wahalhalun Falasdinawa da na Gaza. Akwai rikicin kasar Yemen da kuma na kwana-kwanan nan na kasar Myanmar. Shugaba Buhari ya musalta rikicin Myanmar da abin da ya faru a kasar Bosnia a shekarar 1995 da kuma kasar Rwanda a shekarar 1994.

Saturday

Duk wanda tsautsayi yakai shi ya taba saniya to sunansa gawa : mabiya addinin hindu


“Kowa ya taba saniya, sunansa gawa”

A kasar Indiya wasu mabiya addinin Hindu masu bautar shanu sun lashi takobin kashe duk wani Musulmin da ya yanke saniya a sallar Layya.

A kasar Indiya wasu mabiya addinin Hindu masu bautar shanu sun lashi takobin kashe duk wani Musulmin da ya yanke saniya a sallar Layya.

Tuni shugabannin addinin Islama na kasar Indiya suka fara yi wa mabiyansu hannunka mai sanda, domin su nisanci yanke shanu ko kuma bujumai, saboda guje wa duk wani rikici da ke iya kunno kai a tsakaninsu da masu bautar wadannan dabbobin.

Wasu kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayi sun zargi Musulmai da yi wa allolinsu kisan kiyashi, abinda yasa ‘yan addinin hindu suka fara kai wa Musulmai hari.

Yadda aka yi wa 'shedan' ruwan duwatsu a Mina

Hotunan yadda mahajjata suka jefi 'shedan' a Mina.

Kimanin mahajjata miliyan biyu suke gudanar da jifan shedan a ci gaba da aikin hajjin bana a Mina kusa da birnin Makkah na kasar Saudiyya.


Wani mahajjaci dattijo yana kallon wurin da ake jifan shadan.


Hanyoyi daban-daban da mahajjata suke isa wurin jifan daga bangarori daban-daban a Mina.
<!-- AdSense --!>

Wadansu mahajjata yayin da suka kama hanyar isa Jamarat wato wurin da ake jifan shedan.

Friday

Kenya ta hana samar da leda ko shigar da ita kasar: kokasan dalili.


A ranar Litinin din nan gwamnatin Kenya ta tabbatar da dokar hana shigar da jakunkunan leda ko samar da su a kasar.

A ranar Litinin din nan gwamnatin Kenya ta tabbatar da dokar hana shigar da jakunkunan leda ko samar da su a kasar.
Dokar ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wadanda suka karya ta inda za a ci tarar dala dubu 40 ko daurin kasa da shekaru 4 ga wadanda suka saba dokar.

Kusan tsawon shekaru aka dauka kafin a tabbatar da dokar ta shafi ‘yan kasuwa, masu samar da ledar ko amfani da ita.
Ma’aikatar Kula da Mahalli ts Kenya ce ta kirkiri dokar domin magance matsalar gurbatar mahalli.

Ministan Muhalli Judy Wakhungu ya ce, jakunkunan leda barazana ce ga Kenya kuma dole ne a rabu da su.
Amma masu bincike sun bayyana cewa, sama da mutane dubu 100 ne za su rasa aiiyukansu sakamakon daukar wannan mataki.

Sunday

Bidiyon gwajin tashin jirgi mara matuki na kamfanin Bayraktar.

Bidiyon gwajin tashin jirgi mara matuki na kamfanin Bayraktar da ke Turkiyya.

Sai dai gwajin baiyi Nasara ba.

Duba yadda jirgin ya kasance bayan ya yunkura ya bayyana a sararin samaniya.



GA BIDIYON NAN

(Trt Hausa)

DOWNLOAD HERE

Wednesday

Jami'an tsaro sun harbe wani mutum a fili a kan ya yiwa 'yar shekara 3 fyade: (karanta)

Kalli sauran hotuna.


A can kasar Yemen ne a ka gurfanar da wani mutum da laifin yi wa 'yar shekara 3 fyade sannan kuma ya kashe ta wanda hakan ya sa a ka harbe shi a fili don ya zama izina ga jama'a.



A ranar litinin din da ta gabata ne cikin garin Sanaa da ke kasar Yemen, daruruwan jama'a su ka yi cincirundo don ganin yadda za a harbe wani mutum saboda ya yiwa 'yar shekara 3 fyade kuma ya kashe ta.


An harbe Muhammad Al-Maghrabi mai shekaru 41 a duniya da bindiga kirar Ak47 a
tsakiyar garin Sanaa inda daruruwan jama'a su ka fito kallo.


Muhammad Al-Maghrabi kafin a harbe shi.


Motar 'yan sandan da ta dauko Muhammad zuwa tsakiyar garin Sanaa mai suna Tahrir ta samu rakiyar wasu motocin na 'yan sanda har guda biyar saboda gudun ko ta kwana
don ganin irin yawan jama'ar da su ka fito ganin zartar da hukuncin.

Hhh Hhh Jakuna Da fasa kwaurin Motoci : (karanta)


Ko a wacce kasace??? biyomu





'Yan sandan Afrika ta Kudu sun dakile wani yukuri na fasakwaurin wata mota mai tsada da aka sato zuwa kasar Zimbabwe ta hanyar amfani da jakuna wajen ketarar da ita tekun Limpopo.

Mutanen da ake zargi da hannu dai sun ranci na kare zuwa cikin dajin Zimbabwe, bayan kokarin ciro motar daga turbayar da ta kafe bai yi nasara ba.

A watan Disambar bara ma an samu wata mota da aka sace a birnin Durban a gefen tekun wasu jakuna na janta.
'Yan sanda na bincike ko akwai gungun mutanen da ke da hannu a wannan sabuwar hanyar fasakauri.

Dan sanda Motlafela Mojapelo, ya ce an gano motar kirar Marsandi C220 a kusa da tekun da ba shi da nisa da Musina.
Masu fasakaurin dai sun sanya kwanon rufi a karkashin tayoyin motar ta yadda za a samu saukin curo ta daga cikin yashin da ta kafe.

Kafafen yada labaran kasar sun ambato Mista Mojapelo na cewa, "Mutanen da ake zargi da fasakaurin na amfani da jakuna wajen jan motar domin tsallaka tekun, amma jami'anmu sun isa wurin a kan lokaci suka kuma auka musu, bayan da alamu suka nuna jakunan sun kasa jan motar saboda sun gaji. "
Jakunan dai ba su ji wani rauni ba.
Ba a san dalilin da yasa masu fasa kaurin suka gwammace su yi amfani da jakuna wajen jan motar zuwa Zimbabwe ba, sai dai mai yiwuwa saboda motoci da dama na zamani ana sanya musu wata na'ura da ke amfani da tauraron dan adam wajen gano inda suke idan an sace su.
Kuma na'urar na aiki ne kawai idan ana tuka motar.

Kogin Limpopo na bakin iyakar Afrika ta Kudu da Zimbabwe kuma hanya ce da bakin haure ke amfani da ita wajen zirga-zirga tsakanin kasashen biyu.

Sai dai wakiliyar BBC a Johannesburg, Pumza Fihlani, ya ce batun cewa ana amfani da hanyar a yanzu wajen fasakaurin motoci abu ne mai ban mamaki.

Wakilin ya kara da cewa jami'an tsaro na sintiri a wurin domin hana aikata manyan lafuka.

Tuesday

More Picture's : A karon farko an daura auren wasu kattin maza su biyu masu ikirarin su Musulmi ne a kasar Ingila.






A karon farko an daura auren wasu kattin maza su biyu masu ikirarin su Musulmi ne a kasar Ingila.

Jahed Choudhury dan shekara 24 ya angwance da abokin Luwadinsa Sean Rogan mai shekara 19 a sigar auren Musulunci a kotun daura aure dake Walsall

Hausa times ta ruwaito yan luwadin Biyu sun kasance tare tsawon shekaru Biyu, Bayanai sunce soyayya ta kullu ne tsakanin yan Luwadin a lokacinda Sean ya yi kicibis da matashi Choudhury na kuka cike da damuwa zaune a akan wani Benci a garin Darlaston.

Bayan mista Sean ya lallashi matashin ya bashi gagarumin taimako daga nan sai ya cigaba da yaudararsa ta hanyar bashi kulawa da kaytuttuka har ya koya masa Luwadi.

Duk da cewa iyaye da yan'uwan Choudhury sun kauracewa wannan fasikanci tare da Allah wadai kuma suka ki halartar auren amma hakan bai damu matashin ba domin a cewarsa "Sean yayi masa gata a lokacinda yake cikin matsananciyar damuwa"

Suna masu bayyana cewa sunyi farinciki da auren junansu da sukayi musamman ganin cewa su Musulmu ne domin yin hakan zai nunawa duniya cewa musulunci bai hanasu cika burinsu ba.