Showing posts with label masarauta. Show all posts
Showing posts with label masarauta. Show all posts

Tuesday

Kuma dai: Ganduje ya kafa kwamiti domin sake duba rahoton hukumar yaki da rashawa kan sarkin kano

Gwamna Ganduje ya kafa wata kwamiti domin ta sake duba rahoton hukumar yaki da rashawa kan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II .
Gwamna ganduje

Da farko hukumar sauraron kurafe-korafe da yaki da rashawa tace ta gano sama da naira biliyan 3.4 da aka yi almubazaranci dashi a karkashin Sanusi - An tattaro cewa anyi almubazaranci da kdin ne a tsakani 2014 da 2017 Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti don sake duba ga rahoton hukumar sauraron kurafe-korafe da yaki da rashawa na jihar kan zargin almubazaranci da masarautan Kano tayi da kudi har kimanin naira biliyan 3.4.

Wata majiya ta gidan Gwamnatin Kano ta bayyana ma jaridar Daily Trust cewa an kaddamar da kwamitin ne a ranar Juma’a a sannan kuma an bukaci hukumar da ta fara gudanar da aiki ba tare da bata lokaci ba. A cewar majiyar, wasu mutane daga gwamnatin cikin gida da na waje sun matsa ma gwamnan lamba da ya bari hukumar ta gudanar da aikinta yanda ya kamata.

“A wannan lamarin, hukumar tana iya cigaba da gudanar da bincikenta kuma maiyiwuwa binciken zai iya kai ga dakatar da sarkin kamar yanda hukumar ta bukaci ayi a baya." 

KU KARANTA KUMA: Kwana Casa'in - Kashi Na Sha daya 11 - AREWA24 

Majiyar tace, “Ga dukkan alamu, gwamnatin bata yi marhaban da martanin da sarkin ya mayar ga wasikan da aka tura masa ba, saboda wannan dalilin ne aka kafa kwamitin.”

Babu wanda ya sanyamu mu binciki Sarki Sanusi : Muhuyi magaji

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado hukumar tana aiki ne akan rubutacciyar kara da korafe-korafe da ta samu daga al’umma bisa zargin masarautar da almubazaranci.

Sunusi lamido sunusi

Ya kara da cewa hukumar tana gudanar da aikinta ne da kanta bisa yanda sashi na 8,9 da 15 na dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na 2008 ta tanadar.

Kwana Casa'in - Kashi Na Goma 10 | Cigaban shiri. 🔗

Shugaban hukumar jin korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado a ranar Litinin ya bayyana cewa babu wanda ya tunzura hukumar da ta binciki harkokin kashe-kashen kudaden masarautar jihar.

Rimingado, wanda yayi magana da manema labarai a ofishinsa, yace hukumar bata hada lamarinta da kowa ba a wajen binciken da take gudanarwa kan masarautar bisa zargin kashe kudade ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa hukumar tana gudanar da aikinta ne da kanta bisa yanda sashi na 8,9 da 15 na dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na 2008 ta tanadar.

A cewar shi, hukumar tana aiki ne akan rubutacciyar kara da korafe-korafe da ta samu daga al’umma bisa zargin kashe kudade ba a hanyar da ta dace ba a masarautar Kano a karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen mutane 4 da za su yi sulhu a tsakanin Sarki Sanusi da Ganduje. 

Yace “An soma gudanar da wannan binciken ne tare da umurnin gwamnatin jihar Kano, amman bisa sakamakon ganin yanda al’umman jihanr ke korafi.”

Sunday

Jerin sunayen mutane 4 da za su yi sulhu a tsakanin Sarki Sanusi da Ganduje.

Fadar shugaban kasa ta kafa kwamitin mutane hudu da za su kawo karshen takun saka wajen tabbatar da sulhu a tsakanin Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Fadar shugaban kasa dake garin Abuja ta gayyaci shugabannin biyu a ranar Juma'ar da ta gabata domin neman sulhun ta su kamar yadda kafofin wata labarai na kasar nan da dama suka wassafa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kwamitin mutane hudu da fadar shugaban kasa ta kafa domin warware gabar dake tsakanin Gwamna Ganduje da kuma Sarkin Kano sun hadar da gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a matsayin jagora.

Sauran 'yan kwamitin sun hadar da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma takwaran sa na jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.

Ana iya tuna cewa gwamnatin jihar Kano ta bukaci Mai Martaba Sarki Sanusi da ya bayyana yadda aka waye gari babu kimanin Naira biliyan 3.4 a asusun fadar Kano. Sai dai fadar yayin mayar da martani ta ce abin da ta riska a asusunta bai wuci Naira biliyan 1.89.

KARANTA KUMA: Tana ƙasa tana dabo : Ganduje da Sanusi ba su yi sulhu ba tukunna - Hadimin Ganduje.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, al'ummar jihar Kano sun bayyana mafi kololuwar farin cikin su yayin da aka samu sulhu a tsakanin Gwamna Ganduje da kuma Sarki Sanusi inda a cewar su hakan shi zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma ci gaba a jihar.

Saturday

Yanzu Yanzu: Anyi sulhu a tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya zo karshe Biyo bayan wata matsaya da aka cimma a daren ranar Juma’a a Abuja.



Da farko dai a ranar Juma’a Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga lamarin, biyo bayan kiran da aka yi kan ya sanya baki da kuma yawan kira daga dattawan arewa yayinda rikici tsakanin gwamnan da sarkin ke kara daga hakula a jihar.

Sanya bakin Shugaban kasa a lamarin na zuwa ne kwana daya kafin wa’adin da gwamnatin jihar ta dibar ma sarkin akan yayi bayani game da kudaden masarautar.

A taron sulhun da aka gudanar a daren ranar Juma’a a Abuja, gwamnan da sarkin sun amince sun janye takobinsu don ra’ayin Kao da kuma rage fargaba domin guje ma karya doka da oda.

KU KARANTA KUMA: An Haramata duk wani gangamin taro a kano : Ƴan Sanda. 

Koda dai har yanzu babu cikakken bayani kan abunda ganawar ta kunsa, wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya jagoranci ganawar wacce ta samu halartan yan tsirarun manyan mutane.

SOURCE LEGIT.NG

Tuesday

Ali ya ga Ali: Ga Gwamna Ganguje ga Sarki Sunusi II (Hotuna bayan sallar idi)

A yau Talata, 4 ga watan Yuni ne daukacin al’umman Musulmi a sassa daban-daban na duniya suka gudanar da bikin Eid-el Fitr bayan kammala azumin watan Ramadana.


Jama’a sun tunkari masallatai daban-daban domin cika ibadunsu na Ramadana ta hanyar godiya ga Allah madaukakin Sarki.
Hakan ce ta kasance a jihar Kano inda Sarakuna, manyan yan kasuwa, manyan yan siyasa ciki harda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka halarci Sallar idi.


Sarki Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci bayar da sallar idi a babban masallacin idi da ke Kofar Mata a Kano.
Bayan sun idar da Sallah an gano Gwamna Ganduje tare da Sarkin Kano suna Musabaha cike da farin ciki da walwala.

Wannan shine karo na farko da shugabannin ke haduwa tun bayan kunnowar rikicin masarautar jihar, inda
gwamnan ya kacaccala ta zuwa gida biyar.

KU KARANTA KUMA: Kwana Casa'in - Kashi Na Tara 9 | Cigaban shiri.  🔗

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Fadar mai martaba sarkin Kano ta musanta zargin da hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano keyi mata tare da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II na yin bindiga tare da almubazzarantar da naira biliyan 3.4.

Legit.ng ta ruwaito walin Kano, Alhaji Mahe Bashir ne ya bada wannan kariya ga masarautar a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, inda yace zarge zargen da ake yi ma masarautar basu da tushe balle makama, sa’annan ya bayyana daki daki yadda masarautar ta kashe kudadenta.

SOURCE LEGIT.NG

Wednesday

Babban Dalilin da yasa sarki sunusi II bai halarci rantsuwar Ganduje ba.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya noke ya ki halartar taron rantsar da gwamnan jahar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu daya gudana a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito duk da tsare tsaren da gwamnatin tayi na jera yadda Sarkin tare da sabbin sarakunan jahar masu daraja ta daya zasu zauna, amma Sarkin bai halarta ba, duk da cewa kujerarsa ce ke dauke da lamba 1.

KU KARANTA: Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umarci INEC ta bawa PDP.  

Sai dai ana rashin halartarsa taron baya rasa nasaba da rikicin dake tsakaninsa da gwamnatin jahar Kano, tun bayan da Gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu da zasu yi gogayya dashi, wanda hakan ke alanta kokarin Ganduje na rage masa izza.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa duka sabbin sarakunan da suka hada da Sarkin Rano, Sarkin Bichi, Sarkin Gaya da Sarkin Karaye duk sun halarci taron rantsarwar ta Ganduje a matsayin gwamnan Kano karo na biyu.

Da misalin karfe 10:30 na safe ne Alkalin Alkalan jahar Kano ya rantsar da Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a gaban dubun dubatan magoya baya da yayan jam’iyyar APC da suka halarci taron daya gudana a filin wasa na Sani Abacha.

A yayin da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Ganduje ya sanar da bada ilimi kyauta ga duk wasu masu fama da nakasa yan asalin jahar Kano tun daga matakin Firamari har zuwa matakin gaba da sakandari.

SOURCE LEGIT.NG

Monday

Zaben gwamna a Kano: Ganduje zai gabatar da kundi mai shafi 1,800 a gaban kotu

Ganduje ya shirya kundi mai dauke da shafi 1,800 kuma a shirye yake ya gabatar da shaidu 203 tare da su.

“Mun shirya don nuna ma duniya cewa tabbas an gudanar da zabe na gaskiya da adalci a ranar 23 ga watan Maris, 2019”, cewar lauyan shi Barista Musa Abdullahi Lawan.

KU KRANTA KUMA: Gaskiyar Abin Da Yasa Gwamna Ganduje ke Yakar Sarki Sunusi II.  

Yayin da yake magana bayan ya shirya takardun gwamnan a gaban kotun sauraran karan, Barista MA Lawan, wanda ya kasance daya daga cikin jagoran lauyoyin gwamnan, yace ikirarin da jam’iyyar PDP ta gabatar gaban kotun ba mai inganci bane.

Barista MA Lawan yace zasu gabatar da shaidu 203 wadanda suka kasance masu muhimmanci, zasu kuma fada ma kotun cewa tabbas an gudanar da zabe da kuma cewa jam’iyyar PDP ta gabatar da kara mara tushe.

Lauyan na Ganduje yayi watsi da rade-radin cewa jihar ta tayi amfani da damar yima alkalai sauyin wjen aiki domin shigo da wadanda zasu goya musu baya.

Ya kuma dage cewa akwai kararraki 50 a gaban kotun kuma yawancinsu sunyi ma kotun yawa.

SOURCE LEGIT.NG

Sunday

Gaskiyar Abin Da Yasa Gwamna Ganduje ke Yakar Sarki Sunusi II.

Tun bayan fitowar maganar kirkirar sabuwar dokar masarauta a jihar Kano, jama'a suka fara bayyana cewar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na shirin yakar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a kan dalilan da ba a gama hakikance su ba, duk da dai wasu sun ce yin hakan na da alaka da siyasa.

Ganduje and Sunusi
                           Ganduje and sarki Sanusi II


Yanzu haka bayanai na gaskiya sun fara bayyana a kan dalilan da yasa Ganduje ya tsaga gidan sarautar Kano har gida biyar.
Wata majiya dake da kusanci da gwamnatin jihar Kano ta shaida wa majiyar mu cewar gwamna Ganduje na da masaniyar cewar sarki Sanusi II ya gana har sau biyar da jagoran siyasar gidan Kwankwasiyya, tsohon gwamna kuma sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), domin tsara yadda za a kayar da gwamnatin Ganduje.


Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewar sarki Sanusi II ya umarci hakimai da su goya wa jam'iyyar PDP baya a zaben gwamna da kuma tabbatar da cewar jam'iyyar APC ta fadi a zaben gwamnan jihar Kano.

"Har 'yan uwansa ya tattara ya sanar da su cewar su yi aiki tare da jam'iyyar PDP domin tabbatar da cewar gwamna mai ci bai samu damar yin tazarce ba. Ba iya nan fa ya tsaya ba, sarkin ya yi amfani da kujerar sa wajen tara wa jam'iyyar PDP kudi masu yawa daga wurin abokan kasuwancin sa domin tayi yakin neman zabe duk don a kayar da Ganduje ," a cewar wani jami'in gwamnatin jihar Kano.
Majiyar gwamnatin ta kara da cewa bayan an bayyana cewar zaben gwamnan jihar Kano bai kammalu ba, sarki Sanusi ya tuntubi fadar shugaban kasa, uwar jam'iyyar APC ta kasa da shugabannin hukumomin tsaro domin ganin cewar ba a sake gudanar da zaben kece raini a jihar Kano ba, bisa nuna cewar jama'a sun riga sun zabi Abba, dan takarar jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano
" Ya fada musu cewar za a iya samun barkewar rikici a jihar Kano matukar ba a bayyana Abba Yusuf, dan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba. Amma bayan ya ga cewar ba za a fasa gudanar da zaben raba gardama a wasu mazabu ba, sai ya canja dabara, ya koma zuga shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kano domin kar su bari APC ta samu nasara ," a cewar majiyar.

Majiyar ta ce dukkan wadannan abubuwan da Sanusi ya yi ba boyayyu bane a wurin gwamna Ganduje kuma su ne suka fusata shi har ta kai ya dauki matakin da ake ta cece-kuce a kai.
Da aka tuntubi kwamishinan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Muhammad Garba, domin tabbatar da wannan labari, ya ce bashi da ta cewa a kan dangantakar da take tsakanin sarki da gwamna, tare da bayyana cewar " an riga an kirkiri sabbin masarautu ."

Da aka tuntubi shugaban ma'aikatan sarki, Alhaji Munir Sanusi, ya ce bashi da hurumin yin magana a kan batun, tare da bayyana cewar, " ba ni da hurumin yin magana da manema labarai a kan wannan batu saboda akwai na sama da ni da dama a tsarin fada."

POSTED-BY LEGIT.NG 

Saturday

Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano

Marigayi tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I wanda ya yi mulkin shi daga shekarar 1905 zuwa 1990, kaka ga Sarkin Kano na yanzu, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya yi mulki na shekaru biyar ne kawai, daga baya aka takura shi akan sai ya yi ajiye mulkin. An ce Sarkin ya kasance bai iya gabatar da mulki ba saboda yawan son shiga harkar siyasa da yake dashi, hakan ne ya sanya dole aka cire shi daga mulkin.

Ganduje sunusi Dangote

Alamu sun nuna cewa Sarkin na yanzu, Muhammadu Sanusi II shi ma yana fuskantar irin wannan yanayi, inda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya nuna rashin jin dadin sa akan wasu abubuwa da ya ke yi a jihar.

Hakan ne ya tilasta gwamnatin jihar kirkirar wasu sababbin masarautun yanka guda hudu wadanda za su ragewa Sarkin Kano matsayi a jihar, bayan gwamnan jihar ya aika da dokar gurin majalisar jihar, majalisar ta amince da dokar inda aka kara sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar. Wadanda suka hada da masarautar Bichi, Gaya, Karaye, da kuma Rano.
Wani abin mamaki kuma shine, babu wata kungiya, ko wani babba arewa ko fadar shugaban kasa da ta sanya baki akan lamarin, duk sun barshi ya ji da kansa.

Sai dai kuma, shahararren mai kudin nan na nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote, shi ne kadai wanda ya shiga lamarin, inda ya roki gwamnan jihaar akan kada ya cire Sarkin daga kujerar shi, amma Ganduje ya nuna dole sai ya cire shi.

KU KARANTA: Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi Fita Yawo.  

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar ta ce Ganduje ya bai wa Dangote wasu ka'idoji da dole ne sai an cika su domin ceeto sarkin, tunda har sarkin ba zai daina zagin gwamnatinsa ba.

Majiyar ta ce, "Gwamnan ya gayawa Dangote ya je ya sanar da Sarkin cewa ya zabi abu daya a cikin guda uku da zai gindaya masa: ko ya yi murabus da kansa, ko kuma gwamnati ta cire shi da karfin tsiya, ko kuma gwamnati ta kirkiro wasu sababbin masarautun yanka guda hudu a jihar. Ganduje ya bayyanawa Dangote cewa dole zai aiwatar da daya daga cikin wadannan ka'idoji guda uku da ya gindaya, tunda har sarkin ba zai daina shiga harkar siyasar jihar ba. Amma ba dan Dangote ba da tuni Ganduje ya cire Sarkin daga kujerar shi," in ji shi.

Posted by LEGIT.NG

Wednesday

Sabbin sarakunan da ka nada haramtattu ne, kotu ta rushe sabbin masarautun Kano

Kotun ta bayar da bayar da umarnin rushe sarakunan tare da koma wa karkashin tsarin da ake kai a baya har sai an kammala sauraren karar da aka shigar a kan nadin sabbin sarakunan.

Gov.  Ganduje

A ranar Asabar ne gwamna Ganduje ya nada sabbin sarakunan yanka hudu a jihar Kano biyo bayan amincewa da dokar kirkirar sabbin masarautu da majalisar dokokin jihar Kano tayi.

Tun a ranar Juma'a, kwana daya kafin bikin nadin sabbin sarakunan, wata kotun jihar Kano ta bukaci gwamna Ganduje ya dakatar da gudanar da bikin nadin sabbin sarakan. Amma sai gwamnatin jihar ta bayyana cewar umarnin ya zo mata ne bayan ta rika bawa sabbin sarakunan takardar nada su.

Ganduje yayin mika sandar mulki ga sabon sarkin Bichi; Aminu Ado Bayero
Ana zargin Ganduje da kirkirar sabbin masarautun domin daukan fansar siyasa a kan sarkin Kano Muhammadu Sanusi II domin rage masa karfi da ikon da yake da shi.

Amma gwamnan ya kafe kan cewar babu wata matsala tsakaninsa da sarkin, tare da bayyana cewar ya yi hakan ne domin kishin jihar Kano da cigaban ta.

DUBA WANNAN: Katankatana! Rikicin masarautar Kano ta dauki sabon salo, manyan hakimai 4 sun yi tirjiya. 

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a nadin sarkin Kano da suka hada da - Madakin Kano, hakimin Dawakin Tofa, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, hakimin Wudil, Abdullahi Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Mai Tuta, hakimin Gabasawa, Bello Abubakar da Sarkin Ban Kano, hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan, sun kara shigar da karar gwamna Ganduje da gwamnatin jihar Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano, kwamishinan shari'a na jihar da sabbin sarakunan da aka nada - Tafida Abubakar Ila, Ibrahim Abdulkadir, Ibrahim Abubakar II da Aminu Ado Bayero - na daga cikin mutanen da aka shigar da karar.

News SOURCE LEGIT.NG

Tuesday

Tirkashi : Dogaran Sarkin Kano sun fara gudu daga fadar Kano

Zirga-zirga ta ragu a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, bayan kaddamar da sababbin masarautun yanka guda hudu da gwamna Ganduje ya yi wanda suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Ranar Lahadin da ta gabata fadar a cike take da al'umma a lokacin da sarkin ya dawo daga aikin Umrah, inda dubunnan mutane suka fito suna yi mishi barka da zuwa a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.


KU KARANTA: Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba - Majiyar gwamnatin Kano. 

Mutanen sun biyo shi har zuwa fadar shi daga filin jirgin, inda suke yi mishi kirarin "mai martaba sarki"

Mun samu labarin cewa a yau Talatar nan zirga-zirga ta ragu sosai a fadar, duk yawan zirga-zirgar da aka saba gani a fadar ta mutane da ababen hawa komai ya ragu.
Mutane kalilan ne suka rage a fadar sai ma'aikatan fadar.

Wani Dogari wanda ya yi magana da manema labarai ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewar sarkin ya zabi ya kadaice kanshi tun dawowar shi daga kasa mai tsarki.
Ya ce: "Tun dawowar Mai Martaba, bai sake magana ba. Ya samu ganin baki kalilan ne da suke zuwa ziyartar shi. Manema labarai da yawa sun zo domin yin hira da shi amma ya hana kowa ganinshi.

KU KARANTA: Sabbin sarakuna: Mu na tare da masarautar Kano, al'ummar Wudil sun bijirewa Ganduje. 

"Wannan kirkiro sabbin masarautu ya shafi yawaitar zirga-zirga a fadar nan, kuma ina mai tabbatar muku cewa Mai Martaba bai ji dadin abinda ya faru ba."

A cewar shi, Dogarai da yawa da suke fadar Sarkin Kanon sun bar fadar zuwa sauran masarautun da aka kirkira, musamman ma masarautar Bichi inda dan gidan Marigayi Ado Bayero ke Mulka.

news SOURCE By LEGIT. NG

Monday

Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba - Majiyar gwamnatin Kano

Wata majiyar gwamnatin Kano ta bayyana yadda gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya so ya tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ba don Alhaji Aliko Dangote ya gaggauta shiga tsakani ba.
Ganduje and Sunusi II
Gov. Ganduje And Sunusi II

Majiyar da ta nemi a boye sunanta, ta ce sarki Sanusi II ne da kan sa ya roki Dangote a kan ya lallashi Ganduje ya fasa cire shi daga kujerar sarkin Kano bayan ya fuskanci dangantakar dake tsakanin fada da gwamnati ta lalace sosai.

" Ana fara maganar sake bude binciken zargin badakala da kudin masarauta da kuma batun kirkirar karin sabbin sarakuna, sarkin ya aiko hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote wurin Ganduje domin ya roke shi a kan ya fasa cire shi daga kujerar sarkin Kano .

" Amma sai Ganduje ya shaida wa Dangote cewar ya koma ya sanar da Sanusi II cewar yana da zabi guda uku; ko ya yi murabus da kan sa ko gwmnati ta tsige shi ko kuma ta kirkiri karin sabbin masarautu hudu a jihar.

"Ganduje ya bawa Dangote tabbacin cewar dole gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da daya daga cikin zabin guda uku tunda sarki Sanusi II ba zai daina shiga harkokin nuna adawa da shi a siyasance ba. Ba don Dangote ya shiga tsakani ba, babu abinda zai hana Ganduje ya tube Sanusi, " a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Rikicin masarauta a Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus.

Majiyar ta kara da cewa, duk da hakan ba lallai gwamna Ganduje ya hakura ba gaba daya, akwai yiwuwar ya canja shi zuwa daya daga cikin sabbin masarautu hudu da aka kirkira, sannan ya maye gurbin sa da daya daga cikin sabbin sarakunan da aka nada ranar Asabar.

Daga cikin gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar Kano tayi, akwai batun yin canji a tsakanin sarakuna zuwa kowacce daga cikin masarautu biyar da yanzu Kano keda su. Duk wanda ya gaji sarautar Kano, ta iyaye ko kakanni, zai iya zama sarkin kwaryar birnin Kano.

News SOURCE  LEGIT. NG


Rikicin masarauta a Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus.

Haruna Sanusi, Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano yayi murabus daga mukaminsa, bisa dalili na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan.
Ganduje Ans Sunusi

Hakimin garin, wanda ke rike da mukamin Dan Galadiman Kano, ya sanar da murabus dinsa a wata wasika zuwa ga Sakataren gwamnati, mai kwanan wata 10 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar Kano, a ranar 8 ga watan Mayu ya samar da sabbin masarautu hudu da manyan sarakuna a jihar, inda aka yi zargin cewa yana so ya karya darajar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne.

Legit.ng ta rahoto cewa Sarakunan da aka nada sune; Aminu Ado-Bayero, Bichi; Tafida Ila, Rano; Ibrahim Abdulkadir, Gaya da kuma; Ibrahim Abubakar ll, Karaye.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje   

A ranar Juma’a, wata babbar kotun jihar Kano da ke zama a Ungogo ta yi umurnin hana gwamnan kacaccala masarautar.
Amma a ranar Asabar sai gashi gwamnan ya gabatar da wasikun nadi ga sabbin sarakunan, cewa bashi da masaniya akan umurnin kotun.

SOURCE LEGIT.NG



Sunday

Sabbin sarakuna: Mu na tare da masarautar Kano, al'ummar Wudil sun bijirewa Ganduje

Biyo bayan nadin sabbin sarakunan yanka guda hudu da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a ranar Asabar, wasu kungiyoyin al'umma a karamar hukumar Wudil sun bijire wa masarautar Gaya da suka fada a karkashinta, tare da bayyana mubaya'ar su ga masarautar Kano.
Ganduje and Sunusi

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala taron kungiyoyin al'umma a karamar hukumar Wudil, Malam Muhammad Idris, shugaban gamayyar kungiyoyin tare da sakatarensa, Dakta Baba Sani Wudil, sun bayyana cewar ba a tuntubi al'ummar karamar hukumar Wudil ba kafin a kirkiri sabbin masarautun, a saboda haka an saba wa tsohon tarihin da yankin keda shi.

DUBA WANNAN : Mutane 5 Masu HAtsari a Duniya Da Ake Nemansu Ruwa a Jallo.

" Ba mu nemi a kirkiri sabuwar masarauta ba, kuma da gwamnati tayi niyyar yin hakan ba ta tuntubi jama'ar karamar hukumar Wudil ba. Mun tabbatar da cewar sabuwar dokar masarautun da gwamnati ta kirkira za ta lalata tsohon tarihin da Wudil keda shi.

"Mu na da dogon tarihi a karkashin tsohuwar masarautar Kano a matsayin mu na 'Jobawa', kuma mu na son gwamna Ganduje ya san da hakan.
"Da wannan muke son sanar da cewar dukkan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Wudil su na biyayya ne ga masarautar Kano ba Gaya ba, " a cewar sa.

DUBA WANNAN: Rikicin Kano: Gwamna Ganduje ya ba Sarki Sanusi II zabi guda 3.  

Ya kara da cewa al'ummar karamar hukumar Wudi zasu mika koken su ga dukkan hukumomin da abin ya shafa domin a duba bukatar su.

A cewar sa, masu da ruwa da tsaki a Wudil zasu bi duk hanyoyin da suka dace da dokokin Najeriya domin ganin cewarv sun cigaba da zama a karkashin tsohuwar masarautar Kano ba sabuwar masarautar Gaya da gwamna Ganduje ya kirkira ba.

SOURCE LEGIT. NG

Rikicin Kano: Gwamna Ganduje ya ba Sarki Sanusi II zabi guda 3

Watakila za a kai Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a gaban kotu a game da yadda aka batar da kudin Masarautar kasar a lokacin da ya dare kan gadon sarauta bayan rasuwar Marigayi Sarki Ado Bayero.
Ganduje and Sunusi

Daily Trust ta rahoto yadda Sarkin na Kano ya samu matsala da Gwamna mai girma Abdullahi Umar Ganduje. A cikin makon da ya gabata ne hukumar da ke binciken satar dukiyar gwamnati a jihar Kano ta taso fadar Kano a gaba.

Hukumar tana zargin Masarautar da barnar dukiya don haka ta soma bincike bayan gwamnati ta kuma kirkiro wasu sababbin Masarautu, wanda tuni an nada masu Sarakuna yanzu haka. A cikin mako guda dai duk aka yi wannan.

KU KARANTA: Halittu Guda 5 Da Allah Yayi musu baiwa da tsayin Rayuwa.

A makon jiya ne Isa Sanusi Bayero, wanda shi ne tsohon Sakataren Sarkin Kano, ya bayyana a gaban hukumar da ke binciken fadar Kano. Ana zargin Sarki Sanusi II ne da wawure duk makudan kudin da aka bari cikin asusun fadar.

Rahoton na Daily Trust cewa bayan Sarki ya samu labarin cewa ana shirin maka sa gaban kotu idan an gama bincike ne yayi maza ya ruga wajen Aliko Dangote, wanda ya nemi ya nema masa alfarma wajen gwamna mai-ci Ganduje.

KU KARANTA: Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka. 

Gwamnan ya fadawa Aliko Dangote cewa Sarki Sanusi II yana da zabi har 3; ko kuma ya sauka daga kan gadon sarauta da kan sa, ko kuma a kirkiro sababbin Masarautu a jihar, ko kuma a tsige sa daga kan karagar mulki da karfin tsiya.

A karshe dai gwamnatin Kano ta kirkiro sababbin Masarautu 4 wanda kuma tuni aka nada masu Sarakuna. Ba don sa bakin Aliko Dangote ba, ana tunanin cewa da tuni Mai girma Abdullahi Ganduje ya tsige Sarki Sanusi daga kan mulki.
Sai dai kuma ana tunanin cewa Ganduje zai iya aika Sarki Sanusi II zuwa wata Masarauta a jihar, sannan ya maye gurbin sa da wani daga cikin sabbabin Sarakunan da aka nada a cikin kwananin nan.

SOURCE  LEGIT.NG

Saturday

Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka.

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna sum iiso dakin taro na Sani Abacha Stadium domin bikin karbar takardun sababbin Sarakunan Rano, Bichi, Karaye da Gaya wanda aka basu jiya Jumu'a.

ganduje
Sarakunan hudu da aka yiwa nadin sun hada da; Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila, Sarkin Gaya Alhaj Ibrahim Abdulqadir Gaya, Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II.

KARANTA WANNAN : Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje   

Yayin bikin nadin sarautan, Gwamna Ganduje ya ce sabbin masarautun da aka kirkira za su inganta masarautar Kano.
"Mun san cewa wannan sabbin masarautun za su inganta tsaro da ilimi," a cewar Ganduje.

Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta sanar da ranakun da za a yiwa sarakunan bikin nadi na musamman a nan gaba.

alumma

A baya dai kunji cewar kotu a kano ta dakatar da  gwamnati kan batun nadin sabbin sarakunan, sai dai lokacin da labarin dakatar da gwamnatin jihar Kano da kotu tayi daga kafa sabbin masarautu a jihar Kano, kwamishinan shari’ah na jihar, Barista Ibrahim Mukhtari ya bayyana cewa har zuwa daren ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu, bai amshi wani umurni daga kotu akan lamarin nadin sabbin saranan ba.



READ HERE: Top 5 animal that has the longest life span.  



The vedio from Arewasound-channel.

 Da farko dai an rawaito cewa wata babbar kotun jihar Kano, ta dakatar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga kafa sabbin masarautu hudu da majalisar dokokin jihar ta yi.


Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje

A jiya Juma'a ne wata Kotun Koli a jihar Kano da ke unguwar Ungogo ta dakatar da gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga daukar matakin raba masarautar jihar zuwa gida biyar.
image© legit.ng

Masarautun da gwamnan zai kara guda hudu sun hada da Masarautar Rano, Masarautar Bichi, Masarautar Gaya da kuma Masarautar Karaye.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da Rabi'u Sule Gwarzo ya kai inda yake kalubalantar gwamnan jihar akan yunkurin shi na kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.

Alkalin kotun, mai shari'a Nasiru Saminu, ya ba da umarni ga dukkanin masu hannu a lamarin akan su saurara domin a tabbatar da yiwuwar hakan.

Bayan haka kuma, mai shari'a Saminu, ya ba da umarni ga gwamnan jihar da kuma masu buga takardu na gwamnati akan su dakata da wallafa dukkanin takardu da suke da alaka da sababbin masarautun.
Mai gabatar da karar shi ne Rabiu Sule Gwarzo, yayin da kakakin majalisar jihar ya ke kalubalantar karar.

KU KARANTA: Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka.  A yau Asabar

Bugu da kari, majalisar dokokin Kano ita ce mai kalubalantar kara ta biyu, sai gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin na uku da zai kalubalanci karar, alkalin alkalan jihar kuma kwamishinan shari'a na jihar shine na hudu da zai kalubalanci karar sai kuma masu wallafa takardu na gidan gwamnatin Kano a matsayin na biyar.

Alkalin kotun ya bayyana ranar Laraba 15 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a cigaba da sauraron karar da kuma albarkacin bakin jama'a.
MAJIYA LEGIT.NG

Sunday

Ziyarar Jonathan zuwa kano : see all pictures

Mai girma tsohon shugaban kasar nigeria Dr Goodluck jonathan ya ziyarci Jihar kano a jiya wajen mika ta'aziyyarsa zuwa ga gwamnati da masarautar jihar kano da kuma sauran Al'ummar jihar bisa Rasuwar dattijon arziki Marigayi Dr. Yusuf maitama sule. Tsohon shugaban dai ya bayya maitama sule a matsayi jajirtacce wajen hadin kan al'ummar wannan kasa. Haka kuma tsohon shugaban ya sami tarba daga tsohon gwamna a jihar ta kano Dr. Ml. Ibrahim shekarau da kuma Alhaji sule lamido tsohon gwamnan jihar jigawa dama sauran masu ruwa da tsaki.

KALLI HOTUNAN YAYIN ZIYARAR

Tuesday

Sarkin Kano Sunusi Lamido II Yayi Barazanar Rushe Gidan Kadiriyya : Kano


sunusi lamido ||

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu
Sanusi na biyu ya yi barazanar rusa
shalkwatar Darikar Kadriyya ta Afrika ta
Yamma da ke birnin, muddin ‘ya'yan tsohon
shugaban Darikar marigayi Sheikh Nasiru
Kabara suka gaza wajen hada kawunansu.

Sarkin Sanusi ya yi barazanar rusa gidan Kadiriyya
Muhammadu Sanusi II ya yi wannan
barazana ce lokacin da daya daga cikin
'ya'yan marigayin Nasiru Kabara, Sheikh
Askiya Nasiru Kabara ya ziyarce shi a
fadarsa.

Tun bayan nada sabon shugaban Darikar
Kariballa Nasiru Kabara ake ci gaba da
samun sa-in-sa tsakaninsa da Sheikh
Abduljabbar Nasiru Kabara.

majiyarmu ta samu labarin cewea Sarkin na
Kano ya bayyana takaicinsa ganin yadda
‘yayan na Nasiru Kabara suke rikici da juna,
in da ya bayyana cewa kowanne daga cikinsu
na iya wakiltar mahaifin nasu a maimakon
takun saka da juna.

Sarki Sanusi ya jinjina wa Malam Nasiru
Kabara kan yadda ya ke jagorantar mutane a
lokacin da yake raye

Sannan ya kara da cewa daukan matakin
rusa gidan marigayin don gina masallaci ya
fi alheri fiye da yadda 'ya'yansa ke kokarin
wargaza abin da ya bari.

Friday

Bãnà Tsoron barin mukamina indai Akan fadin gaskiyane : Sarki sunusi II Na kano.





Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu
Sunusi II ya gargadi shugaban kasa Muhammadu
Buhari da yayi taka tsantsan da fadawansa na
fadar gwamnati, don kuwa tamkar masu amshin
shata suke.


Sarkin yayi wannan gargadi ne a ranar Alhamis
23 ga watan Maris a taron tunawa da babban
lauyan Kehinde Sofola a jihar Legas, inda yace
yan amshin shata sune asalin makiyan shugaban
kasa Muhammadu Buhari, kuma idan bai bi a
hankali dasu ba, zasu lalata duk wani kokarin
dayake yi.

Sarki ya shawarci Buhari da kada ya dinga
kyamar masu sukar gwamnatinsa “Ina tausayin
masu rike da madafan iko, saboda a koda yaushe
zagaye suke da makiya” ,
Sarki yace ya shugaba
Buhari na bukatan mutanen da zasu dinga fada
masa gaskiya komai dacinta.

Sunusi yace dalilin daya sa ya fallasa badakalar
sama da dala biliyan 20 a zamanin gwamnatin
tsohon shugaban kasa Goodluck shine saboda
baya tsoron barin kujerarsa, saboda ya san ba zai
dawwama a kujerar dindindin ba.


Sarki yace wasu mutane suna tsoron fada ma
shuwagabanni gaskiya ne saboda gudun kada a
sallame su daga aiki, “duk mutanen da ake tsoron fada ma gaskiya suna ina ne yanzu? Don haka
wadanda suke kan mulki suma su tuna mulki mai
wucewa ne.”
inji shi

Mai martaba ya cigaba da fadin cewa baya
ruduwa idan fadawa suna fada masa cewa zai
dawwama a kan mulki, don haka ne ma baya
tuntubarsu dangane da muhimman shawarwari,
sa’annan dalilin daya sa ya daina sukar shugaba
Jonathan shine saboda ya bar mulki, don kuwa
idan na kan mulki ne zaka fada masa gaskiya.

“idan kana son zama dan kasa na gari, toh ka fada
ma gwamnati mai ci gaskiya”.


Dayake bada labarin yadda ya bar kujeran
gwamnan CBN, Sunusi yace “Dole dai wata rana in
bar kujerar gwamnan CBN, zan iya mutuwa, wa’adin
mulki na ka iya karewa, ko kuma a tsige ni, bani
da iko kan wannan. Don haka ban yi mamakin
sallama tab a, na san a rina, saboda an taba
umarta ta da inyi murabus, amma naki ya.

“Amsa daya na basu, kace in yi murabus saboda
na fada maka an saci kudi, sai dai ka fara fada ma
ministan tayi ritaya.

“Mutane sun manta cewa wannan gwamnan ko
shugaban kasa da kake jin tsoron fada ma gaskiya
zai bar kujerarsa wata rana, abinda kawai za’a iya
tunaka da shi a kai, shine yadda ka tafiyar da
rayuwarka a lokacin da kake raye.”
Inji mai matarba Sarki