Tsohon kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Metuh, ya koka kan yadda aka rinka yi masa barazana har dai daga karshe ta kai aka cafke shi sakamakon wata caccaka da ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya kira sa da " Shugaban da ke aikata zunubi ba tare da yafiya ba."
Metuh ya bayyana hakan a lokacin da yake bayar da hujjoji a matsayin hujja na 15 a karar da aka shigar akansa tare da kamfaninsa mai suna 'Destra Investment Ltd', bisa zargin aikata laifuka 7 na karbar kudin makamai daga hannun Sambo Dasuki a shekarar 2014 da suka kai N400m, karar da aka shigar a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Ametuh ya ce a lokacin da ya ke matsayin sakataren watsa labarai na PDP a watan Disamba 2015, ya mayarwa APC wani martani inda ya sanar da 'yan Nigeria ' cewar wannan gwamnatin za ta iya kamawa tare da tsare kowanne dan Nigeria' wanda ya sa ya kira shi (Buhari) da suna 'Shugaban kasar da baya tankwasuwa akan laifuka,
Metuh ya ce sanarwar"ta sanya aka fara yi min barazana da kuma gargadi a wurare daban daban daga gwamnati, inda suka tabbatar da cewa 'ba za su ragawa Olisa Metuh ba, sakataren watsa labarai na PDP'."
Ya ce tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wanda ya jagoranci wata tawaga ta gwamnatin tarayya zuwa wani bukin bisne gawa a jihar Ebonyi, ya yi masa barazana a gaban wasu dattawan PDP daga shiyyar Kudu maso Gabas cewar lalallai ne gwamnatin tarayya ya shirya koya masa darasi.
Tun farko, mai shari'a Okon Abang ya ki karbar korafin lauya mai kara, Sylvanus Tahir, na kada kotu ta amince da duk wasu bayanai da Metuh ya gabatar.
An dage sauraron karar har zuwa 26 zuwa 30 ga watan Nuwamba.
No comments:
Write Comments