Tuesday

Home Jam'iyyar NRM Tasha Alwashin Baiwa Gwamna Ganduje Kuri'a Miliyan Daya A Zaben 2019'
Image result for GANDUJE
KHADIMUL ISLAM GWAMNA  ABDULLAHI UMAR  GANDUJE
Jam’iyyar NRM reshen jihar Kano ta bayyana cewa za ta marawa Gwamnan jihar Kano Dakta, Abdullahi Umar Ganduje da sauran ’yan takarar Sanatoci uku na jam’iyyar APC don kai wa ga nasara a zabubbukan shekarar 2019 mai gabatowa.

Shugaban jam’iyyar na Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi Bichi ya bayyana haka a yayin taron jam’iyyar da shugabaninta na kananan hukumomi 44 na jihar Kano da aka yi ranar Lahadi a dakin taro na cibiyar nazarin Dimokradiyya da aka fi sani da gidan Mambayya a Kano. Shugaban jam’iyyar a jawabinsa ga mahalarta taron ya ce bayan tuntubar bangarori daban-daban da suka yi don duba wace alkibla za su bi, sun kai ga matsaya kan su marawa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau tare da sauran sanatocin na Kano ta kudu da ta arewa baya domin tabbatar da sake samun nasararsu. Alhaji Nasiru Abdullahi Bichi, Galadiman Bichi ya yi nuni da cewa ba sun zabi marawa shugaba Buhari baya bane saboda addini ko kasancewarsa dan arewa ba, sai dai don zai fidda al’umma daga halin da jam’iyyar PDP ta jefa al’ummar kasar nan a ciki a mulkinta na baya wanda ta kai duk inda mutum zai shiga sai an caje shi musammam a jihar Kano da sauran wasu jahohi na Arewacin kasar nan.


Ya ce, masu cewa Buhari bai yi komai wajen ci gaban kasar nan ba, karya suke domin ba don zuwan Buhari mulki ba da albashi ma da za a bai wa ma’aikata ya gagara a kasar nan, wanda a lokacin PDP ana fitar da kudade da sunan za a yi wasu ayyuka amma ba a ganinsu, wanda an taba fitar da milyoyin kudi da sunan za a sanya kyamarar tsaro a kasar nan, amma ba a sa ba, da sauran ayyuka da dama da aka fitar da kudin amma ba a yi aikin ba.


Ya ce, ’yan Nijeriya su yi karatun ta natsu su zabi jagorori da suka yarda da su ta ba su kuri’arsu, wannan tasa jam’iyyar NRM a jihar Kano za ta bada goyon bayanta ga Gwamna Ganduje wajen cika alkawarin da ya yi na samawa Buhari kuri’a 5,000,000 ta bada kuri’u 1,000,000 daga jam’iyyarsu ta NRM da take da dinbin magoya baya a jihar ta Kano.

Ya ce, fitina da take tasowa a kan batawa  Ganduje suna da ake ba za ta sa su karaya ba, za su bai wa Gwamnan goyon baya da zai kai ga nasara, haka ma za su bai wa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau goyon baya don zama Sanatan Kano ta tsakiya saboda irin yanda ya tafi da mulkin Kano da ya yi gwamna,  bai taba ragewa kananan hukumomi kudinsu ba, ya kyautatawa ma’aikata, ya bai wa ’yan siyasa dama sun amfana ba kawai yan jam’iyyarsa ba wancan lokacin.

 Alhaji Nasiru Abdullahi Bichi ya kara da cewa wannan marawa Shugaba Buhari da Gwamnatin Kano baya matsaya ce ta uwar jam’iyyarsu da suka yanke cewa duk wani mai nagarta za su mara masa baya shi ya sa suka ga ba wanda ya kai Buhari suka kuma yanke shawara a nan jihar Kano cewa za su mara wa APC don kai wa ga nasara.

Shi ma a nasa jawabin wanda ya wakilci Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau a wajen taron. Mataimakinsa na musamman a kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Yarima ya nuna farin cikinsa da wannan matsaya da jam’iyyar NRM ta dauka na mara musu baya tare da jaddada cewa sun gamsu kwarai da manufofinta na kawo ci gaba.

Alhaji Lawan Yarima ya bayyana irin gamsuwar da yake da ita da tarbiyya da manufa ta NRM da ta shirya irin wannan muhimmin taro wanda a cikinsa ba wata hayaniya da aka taru aka fadi manufofi daidai irin tarbiyar da Sardaunan Kano yake akai, don haka Sardaunan Kano yana tare da NRM tare da rokon yan jam’iyyar da sauran al’umma su fito su marawa Buhari da sauran yan takarar APC baya don kai wa ga nasara a zabuka masu zuwa. A yayin taron dai wakilai daga bangarorin siyasa da kungiyoyi daban-daban sun gabatar da jawabai.


Read More at: LEADERSHIPAYAU.COM
No comments:
Write Comments