Kamar yadda a ke sa rai, tuni dai jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsayar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin dan takararta wanda zai tsaya ma ta a babban zabe mai zuwa na 2019. Hakazalika mafi yawan manazarta na hasashen cewa, shi ne din dai zai sake lashe zaben, duk da cewa babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta kawo wa APC din babbar barazana ta hanyar tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, takara, inda zai kara da shugaban kasar.
To, amma babban abin dubawa shi ne, a yanzu dai dukkan nazari ya nuna cewa, yankin Yarabawa na Kudu maso Yamma su ne su ka fi juya akalar gwamnatin ta Buhari a karkashin jagorancin uban APC na kasa, wato Bola Ahmad Tinubu.
Don haka mafi yawa ke ganin cewa, tamkar a yanzu Kudu ce ke mulkin Najeriya, domin su ne ke da fada-a-aji a cikin gwamnatin. A bisa al’adar siyasar Najeriya da kuma lissafinta, hakan ya na nufin cewa, idan Buhari ya zarce ya kammala mulkinsa a 2023, to mulki zai koma Kudu kenan, inda a ke sa ran cewa, zai mayar wa yankin na Yarabawa mulkin kasar ne. Wato kenan idan hakan ta faru tamkar Yarabawa za su yi mulki na shekara takwas sau biyu kenan.
Ma’ana; sun juya gwamnatin Buhari kamar waina, sannan kuma za su amshi mulki daga hannunsa.
Abin tambaya a nan shi ne, shin idan Buharin ya zarce, to mene ne makomar yankin Arewa kenan, idan wannan hasashe da a ke yi ya zama gaskiya? Lallai kenan Arewa ta na bukatar yin dogon nazari kan abinda ke shirin faruwa. Shin Buhari zai butulcewa Yarabawa ne idan ya zarce ya ki yarda da cigaba da biye mu su kamar yadda ya ke yi a yanzu ko kuwa ’yan Arewa za su zabi Atiku a karkashin tutar jam’iyyar PDP ne, don su san gwamnatinsu za a yi? Wannan ita ce tambayar da mu ke tsammanin duk dan Arewa zai yi kokarin neman ya amsata. Dabara ta rage wa mai shiga rijiya!
Read More at: LEADERSHIPAYAU.COM

No comments:
Write Comments