Thursday

Home Hukumar Soji ta bayyana Iyakar adadin dakarunta da suka mutu a harin Metele
Hukumar Sojin Najeriya ta ce dakarunta guda 39 suka rasu a harin kwana-kwanan nan da mayakan Boko Haram suka kai a Metele ba 188 kamar yadda kafafen yadda labarai suka ruwaito ba.
SOURCE : LEGIT.NG

Wata sanarwa da Birgediya Janar Sani K. Usman ya fitar a madadin hafsan hafsoshin sojan kasa Laftanal Tukur Burutai ta ce dakarun soji Najeriya 53 ne suka jikkata sakamakon harin.

An samu koma baya cikin yakin da sojin Najeriya keyi da 'yan Boko Haram cikin kwanakin nan bayan 'yan ta'addan suna ta kai hare-hare a sansanin sojin cikin makonni biyu.
Kungiyar Islamic State in West Africa (ISWA), wata bangare na kungiyar ta Boko Haram ta dauki nauyin harin da aka kai a Metele.
Duk da cewa hukumar sojin ta amince da afkuwar harin, ta ce anyi kuskure wajen ruwaito adadin sojojin da suka mutu a kafafen yada labarai.

Usman ya ce a duk harin da 'yan ta'addan suka kai, dakarun sojin sun dakile harin kuma sun kashe 'yan ta'adda masu yawa.
Ya ce tun a shekarar 2015, Sojojin Najeriya sun karya gwiwar mayakan na kungiyar ta'addancin na Boko Haram.

Wani bangare na cikin son da Usman ya fitar: "Yan ta'adan sun kai hari a sansanin soji da ke Kukawa, Ngoshe, Kareto da Gajiram cikin makonni biyu daga 2 - 17 ga watan Nuwamba. Dakarun soji sunyi kokarin dakile dukkan hare-haren kuma sun kashe 'yan ta'adda da dama. Sai dai soji 16 sun rasu sannan 12 sun jikata kuma suna asibita suna samun kulawa.
"Kamar yadda kuka sani 'yan ta'adda sun kai hari sansanin sojin Najeriya da ke Metele a ranar 18 ga watan Nuwamba. Dakarun Soji 23 sun mutu sannan 31 sun jikkata kuma tuni an garzaya da su zuwa asibiti. Hukumar Sojin Najeriya tana mika ta'aziyya ga dukkan iyalan sojojin da suka rasu kuma za ta cigaba da bayar da tallafi domin ganin an kawo karshe ayyukan ta'addancin. "
No comments:
Write Comments