Showing posts with label fadakarwa. Show all posts
Showing posts with label fadakarwa. Show all posts

Saturday

Wanene Qassem Suleimani - Dr, Sani Umar Rijiyar Lemu

Wanene Qassem Suleimani - Dr, Sani Umar Rijiyar Lemu : Download mp3

Wanene Qassem Suleimani - Dr, Sani Umar Rijiyar Lemu : Download mp3

DARASI

MAUDU'I Siyasar Kasashen Larabawa, z@luncin Kasar Iran da Amurka da ta@ddancin Janar Qassem Suleimani

GABATARWA  Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu

Malamin yayi cikakken bayani da fashin baki akan siyasar duniya musamman gabas ta tsakiya, da tasirin Kasar Iran, da irin zalunci da ta@ddanci da barnan da shugaban sojojin Iran Janar Qassem Suleimani yayi a doron kasa kafin hallakarsa

Malamin yayi cikakken bayani akan alakar sirri dake tsakanin Amurka da Iran da irin yadda suke taimakon juna

-Ina wanda ke son sanin dalilin da yasa Amurka ta kashe Qassim S#leimani, da kuma shin za'a iya yin yaki tsakanin kasar Amurka da Iran?

-In wanda ke son sanin irin ta@ddancin da Kasar Iran take yi a Kasashen Musulmai da yadda kasashen turawa suke yiwa yaransu da suka raina?

-Ina wanda ke son sanin waye shugaban sojojin juyin juya hali na Kasar Iran Janar Qassim Suleimani da irin mugun ta@ddancin da yayi a doron duniya kafin ya hallaka?



DOWNLOAD NOW

@Arewasound

Sunday

INEC : YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .

YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .


Zaben 2019, Gen Buhari, Dr Atiku


Yau saura kwanaki 2 kacal wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na kowane mai son yin za6e a 2019 ya garzaya maza6ar da yayi rajista domin tabbatar da sunan sa. Tare kuma da kai korafin sa a cibiyar mazabar sa (ward center) idan bai ga sunan sa ba, ko kuma akwai matsala a sunan na sa.

GA DAMA TA SAMU !

Idan ba ka da iko na zuwa mazabar ka domin duba sunan ka, to za ka iya amfani da wayar ka domin duba sunan ka.

Ga yadda abin ya ke :

HANYA TA FARKO

1 - bude manhajar ka ta Opera ko UC Browser sai ka yi bincike ta Google a wannan adireshin :
Voters.inecnigeria.org

Akwai bayanan katin zaben ka da za a nemi ka cike a wannan shafi :

i- sunan jihar ka,
ii- sunan mahaifin ka,
iii- sunan ka,
iv- kwanan watan haihuwar ka (date of birth).

MISALI :
i- KANO
ii- MUHAMMAD
iii- IBRAHIM
iv- 01-10-2000.

KO KUMA :

(i) sunan jihar ka,
(ii) sunan ka (First name),
(iii) lambobi biyar NA KARSHEN VIN ( Voter's Identification Number ) da ke a cikin katin zaben ka, (kana kuma iya sa su gabaki daya).
Sannan ka aika.

MISALI :
i - KANO
ii - IBRAHIM
iii- 01234.

HANYA TA BIYU

2 - ka aika da sunan # Jihar ka, da # Sunan ka, da kuma lambobi 5 na kashe a VIN naka dake a cikin katin zaben ka zuwa ga WANNAN LAMBA :
20120, ko kuma: 08171646879.

MISALI :
KANO
IBRAHIM
01234
zuwa ga 20120, ko 08171646879.

Allah Ya bada sa'a.

A TUNA CEWA KATIN ZABEN KA SHI NE MAKAMIN KA WAJEN FATATTAKAR DUK SHUGABAN BA YA KYAUTATA MAKA, TARE DA ZABEN WANDA KAKE SO YA SHUGABANCE KA.

Allah Ya yi mana zabi mafi alheri. Ameen.

Wednesday

Tofa!! Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

Hamshakin mai kudin ya bayyanawa matasan hakan a lokacin da ya yi wata hira ta musamman da mashahurin mai kudin nan dan kasar Sudan, Mo Ibrahim a Abidjan, babban birnin kasar Kwaddibuwa, a karshen makon da ya gabata.

hamshaki dangote

Wani wanda ya halarci taron ya yiwa Dangote wasu tambayoyi, inda ya ke tambayar shi wane fanni zai fi mayar da hankali inda ace shi matashi ne dan shekara 21 a duniya, sannan kuma yana da sha'awar fara kasuwanci?

Attajirin ya ce zai fi mayar da hankalin shi akan harkokin sadarwa na zamani da kuma fannin noma.

"Wadannan su ne bangarori biyu da za su fi kowanne bangare kawo riba," in ji Dangote.

Sannan kuma mai kudin ya shawarci matasa akan irin dabi'un da suke da su bayan sun fara kasuwanci, musamman ma matasa na yankin Afirka.

Ya ce, "Matasa su na kashe ribar da ba ta zo hannunsu ba idan suna kasuwanci."

"Daga mutum ya fara kasuwanci kuma ya fuskanci kasuwancin yana samun cigaba, maimakon ya yi ta kara jari, sai kaga mutum ya kashe ribar kasuwar a tunanin shi na cewa ribar za ta cigaba da zuwa," in ji attajirin.

KU KARANTA: Yadda aka kama wasu mutane 3 yayin da suke yunkurin tono gawa daga kabari. 

Dangote ya ce, "Idan mutum ya sayi manyan abubuwa na kyale-kyale da more rayuwa, za su dauke masa hankali daga harkokinsa na kasuwanci."

Mai kudin ya bada misali da kansa, in da ya ke cewa, "a yanzu haka bani da wani gida da nake zuwa domin na shakata, wanda ya ke mallakina a fadin duniyar nan."

"Amma kuma akwai da yawa daga cikin masu yi mini aiki da suke da gidajen shakatawa a birnin Landan." in ji Dangote.

Alhaji Aliko dangote dai shine mutum na daya da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Dangote cikakken Bahaushe ne, wanda ya fito daga jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya. Tun lokacin da ya zama na daya a nahiyar ta Afirka har yanzu ba a samu wani wanda ya ko kama kafarshi ba a nahiyar.

To sai dai kuma ba kasafai aka fiya samun masu kudi suna fitowa fili suna ba wa mutane shawarwari ba musamman masu kudi na nahiyar Afirka.

SOURCE LEGIT. NG

Monday

Hukumar Raba Hasken Lantarki za ta fara tilasta sayen mita kan naira 36,991.50

Hukumar Raba Hasken Lantarki ta Kasa (NERC), za ta fara tilasta yin amfani da mita daga ranar 1 Ga Mayu.
meter wutar lantarki

Jami’in Hulda da Jama’a na NERC, Usman Arabi ne ya bayyana haka, tare da cewa za a fara raba mita ga jama’a a karkashin tsarin MAP, wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi.
Ya ce tsarin raba hasken lantarki ta Sashe na 4(3), ya bukaci kowa ya yi amfani da mita domin a rage matsalar da ake fuskanta.

Top3

Arabi y ace masu amfani da wutar lantarki daga Kamfanin AEDC na Abuja da kuma JEDC na Jos, za su iya samun mita bayan kwanaki goma kacal da biyan kudin mitar.
Ya ce kowa har gida za a je a daura masa ta sa.

DUBA WANNAN : Yanzu-yanzu: Gobara a babban filin jirgin sama (Bidiyo) 
“MAP za su caji naira 36,991.50 ga wanda zai daura layin wuta daya tilo a gidan sa. Shi kuma wanda zai daura layi biyu, to zai sayi mita mai layi uku a kan kudi naira 67,055.85.
Arabi ya ce mitar ta yi tsada ne saboda an hada “farashin ta har da ladar aikin kaiwa har gida, daurawa, ladar zuwa a gyara maka idan ta lalace, ko kuma a canja maka wata idan ba za ta iya gyaruwa ba.”

Tuesday

Asalin tsafi : kissar Haruta Da Maruta.

QISSAR HARUTA DA MARUTA

.

Asalin tsafi.

.
Shin Mala'iku Ne Su Ka Koyar da Tsafi?

Kissar Haruta da Maruta, Haruta da Maruta, Tsafi, Aslin tsafi, Tauraruwa zara


Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, Masu Yin Ruq'yah Da Harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700.

Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci sunayen Haruta da Maruta sau daya a cikin Alqur'ani mai girma, acikin Suratul Baqarah.

Ruwayoyi da dama sun zo akan Qissar wadannan sunaye na Mala'iku ko kuma Sarakuna amma dai za mu dauki jigon ruwayar da Ahmad ya fitar acikin Musnad, da kuma ibnu Hibban aciki Sahihinsa daga ibn Umar رضي الله عنهما
sai mu shigar da bayanin sauran ruwayoyin a ciki.
..

Ga cikakkiyar Qissar :

.Lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam ﻋﻠﻴﻪ السلام
daga Aljanna zuwa kasan duniya, sai Mala'iku suka dinga cewa "Ya Ubangiji, yanzu ka sanya wadanda za suy 6arna su dinga zubar da jinin junansu a duniya?!, alhali mu muna girmamaKa tare da gode maKa kuma muna kaskantar da kai a gareKa?".

Sai Allah Ya ce "Ni Na san abinda baku sani ba".

Sai su ka ce "Ya Ubangiji mu fa mun fi yi maKa biyayya sama da 'yanAdam, inda mu ne ka saukar da  mu duniya to ba za mu sa6a maka ba".
Sai Allah Ya ce musu "To ku kawo Mala'iku guda biyu a cikinku. Sai Mu saukar da su kasan duniya, don Mu ga yadda za su yi. (za suyi biyayya ko ba za suy ba?!)".
Sai suka ce "Ya Ubangiji Ga Haruta da Maruta mun za6e su a kaisu"

.
Sai aka saukar da wadannan Mala'iku biyu zuwa duniya, aka sauke su a garin Babila.

Lokacin da aka sauke su sai aka ce musu ga Tsafi nan ku dinga koyawa mutane amma duk wanda ya zo zai koya ku gaya masa in ya aikata ya zama kafuri.

A wata ruwayar kuma an ba su Sihiri ne domin su dinga yiwa mutane gargadi akan su guje shi kada su aikata shi.

To bayan an saukar da su sai Allah Ya mayar da Zahr', wato wannan babbar tauraruwar da muke gani a kuma da wata, sai aka mayar da ita siffar mace.

Sai ta zo wajensu a sura kyakkyawa.

 Da su ka ganta sai su ka nemeta. Sai ta qi amincewa ta ce musu "Saidai in za ku kafurta to zan yarda da ku".
Da su ka ji haka sai su ka ce basu yarda ba.

Sai ta fi, ta sake dawowa da wani jariri a hannunta. Sai su ka kuma nemarta. Sai ta qi amincewa,  ta ce "Saidai in za ku kashe wanan yaron, to zan ba ku hadin kai".

Sai su ka ce basu yarda ba. Sai ta tafi, ta sake dawowa da tukunyar giya a hannunta.

Suka nemeta. Sai ta ce bata yarda ba sedai in za su sha giya tukuna. Sai su ka yarda su ka sha giyar.

Bayan sun sha sai maye ya kama su, su kayi zina da wannan matar sannan kuma suka kashe wannan jaririn.

Lokacin da suka farka sai Allah Ya tambayesu alqawarin da sukayi akan ba za su sa6a masa ba.

Daga nan sai aka ba su za6i akan su za6i irin azabar da  za ayi musu. Shin a duniya suke so ayi musu azaba ko kuma a bari sai an je Lahira?!.
.
Sai suka ce ai azabar Lahira bata karewa, mun za6i ta duniya.

Shikenan sai aka kai daya inda rana take 6ullowa. Kullum idan rana ta 6ullo sai ta tafasa masa kansa.

Dayan kuma sai aka kaishi inda rana take faduwa, kullum in rana zata fadi sai ta kona shi.

Ita kuma Zahra' sai aka mayar da ita tauraruwa ta koma sama.
.
To a lokacin ne aka ba su sihiri, (bisa sa6anin ruwaya).

Sai aka ce duk wanda ya zo yana so su koya masa.

Sai suka dinga koyawa mutane da Aljanu yadda ake raba tsakanin miji da mata amma basa koyawa kowa sai sun ce masa "Tabbas mu fitina ne!, don haka kada ka kafurta".

In Mutum ko Aljan ya yarda zai kafurta sai su koya masa.

Daga nan sai harkar Sihiri da tsafi ta yadu a tsakanin mutane da Aljanu.
.
Malamai sun yi raddi sosai akan wannan qissa musamman kasancewar Mala'iku basa sa6o da kuma maganar cewa su ne suka koyar da tsafi sannan ruwayoyin yawanci Isra'iyliyyat ne, sedai abinda aka samu na 6angarorin qissar daga Alqur'ani da kuma ruwayar ibnu Umar daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
kamar yadda muka ambata.
.
Harkar Bokanci, Sihiri, Tsafi, Surkulle, Rufa-ido, Tsibbace-tsibbace da makamantansu, sun samu shahara sosai da kar6uwa a wajejen aiko Annabi Sulaiman عليه السلام
shi yasa ya zamto yana daga cikin manyan abubuwan da Annabi Sulaiman yay fada  da su kuma ya yaqi masu aikata shi.

Sannan wannan harka ta samu kar6uwa ne da matsayi da shiga zukatan al'umma a wajenjen zamanin Annabi Musa عليه السلام،
inda a lokacin ake ganin wanda ya iya sihiri tamkar wani shugaba kuma wani abin ay wa biyayya sannan abin tsoro.

Za mu kawo cikakkiyar qissar yadda Annabi Sulaiman عليه السلام ya yaqi masihirtan zamaninsa da kuma dalilin da yasa bayan ya  yi wafati Shaidanu suka ce ya mulki duniya ne ta hanyar tsafi.
.
Sannan za mu sake duba qissar Haruta da Maruta tare da bayanin yadda Annabi Musa ya fuskanci matsafan zamaninsa.
.
Duk wannan zai zo insha Allahu a cikin posting din mu mai taken "ASALIN TSAFI", Domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin Suratuz Zariyari cewa:
.
ﻓَﻔِﺮُّﻭﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻭَﻻ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬﺎً ﺁﺧَﺮَ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻣَﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻣِﻦْ ﺭَﺳُﻮﻝٍ ﺇِﻻَّ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﺎﺣِﺮٌ ﺃَﻭْ ﻣَﺠْﻨُﻮﻥٌ ‏[ ﺍﻟﺬﺭﻳﺎﺕ :50 - 52] .
.
Ma'ana:
 "Kamar haka ne (Su wadannan mutanen) babu wani Annabi da ya zo wajen wadanda suka gabace su face sai sun ce masa mai Sihiri ko kuma mai hauka".
.
Wannan ayah tana nuna cewa tun zamanin Annabi Nuhu  ﻋﻠيﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
duk da cewa shi ne farkon Manzanni, duk Annabin da Allah Ya aiko sai Kafurai sun ce masa mai sihiri ne. Kenan tun a lokacin ana yin sihiri.

Wasu Malaman kuma suna ganin sihiri ya samo asali ne daga hannun Aljanu kuma dalilansu sun fi karfi gaskiya.

Insha Allahu za mu cigaba da kawo muku bayanai masuamfani, zasu zo nan gaba kadan da yaddar Allah.

Sunday

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.



* Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayinneman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayintaakan abunda yake wajibi ko mustahabbi akan ka;kamar neman zabin Allah akanyin azuminramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitarda zakka,azumin alhamis da litimin da dai sauransu.

* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan suncikaro, misali: mutum ne yake son yaje umra karona biyu a lokaci guda kuma yana so yaje watakasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allahakan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.

* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikinlamarin sa, to ba zai yi nadama ba Insha Allah.Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].

* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yanakoya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) acikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkunta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibati amrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaana thumma raddini bihi."
Da Harshen Larabci

MA'ANA

"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshenlamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]

* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannankarantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafankarya don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace

* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.

* Wannan Addu'a ta istarawa ana yin tane bayanka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].

* Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah.

* Haka kuma babu wani hadisi da yazo dagaAnnabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masabayani al-amarinsa.

* Babu shakka duk wanda yayi zai samu natsawucikin abunda Allah madaukakin sarki ya zabamasa.

* Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutanedayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayinnutsuwar zuciya, idan aure ne sai kajizuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar.

* Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita nedaga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Anayin tane koda lokacinda aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana dagacikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili".

* Wannan kenan don gane da abunda ya shafiSallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Ayki Abundamuke rubutawa da karantawa Ameen.

ALLAH YA TAIMAKE MU Ameen