Showing posts with label labarai. Show all posts
Showing posts with label labarai. Show all posts

Thursday

Open Facebook Account With Invisible Name, Yadda Zaku Bude Fb Account Ba Tare Da Suna Ba.

Barka da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya.

Yau muna tafe da bayani akan yadda zaku bude FACEBOOK ba tare da suna a jiki ba.

Step 1) Da farko ku bude wannan link http://facebook.com a wayoyinku na android, sannan ku danna Create New Account.


Step 2) Sai ku canja yaren English  Zuwa Yaren Tamil language. Kamar yadda kuke gani a hoton kasa

To Yanzu sai ka nutsu da kyau,, Sannan kabi wadannan steps a nitse , da kuma screen shots  da zaka gani.


1) invisible name fb account text code : wato sunan da zakayi amfani dashi a wajen first name.

 ---->ゖゖ 💟@() ゖ ✔<----

Yanzu kayi copy na wannan code dake sama wanda yake tsakani Arrows (between arrows-->__<--) Sai kayi paste a wajen first name.

2) Yanzu sai ka saka lambar wayarka a email box. Kayi amfani da lambar da ba'a taba bude fb account da ita ba. Sannan kar kayi amfani da email, lambar wayarka kawai zaka saka a email box.

3) kayi selecting na Gender.


4) ka cike date of birth.


5) ka cike wajen Password { ka zabi secure password. Wanda yake da capital latter, Lambobi hade da special word kamar su @ $ # : ! ?.}

Step 3) Bayan ka gama ciccikewa sai ka danna Sign Up. Duba wannan screen shot ! 

Bayan ka dannan singup Zasu turoma da Confirmation Code zuwa lamar da ka saka . Sai kayi amfani da code din kayi comfirm na account naka.


BAYAN DUK KAGAMA WANNAN SAI KA MAIDA YAREN YA KOMA ENGLISH.

Ga yadda zakaga sabon account naka wanda ba suna.


Shikenan yanzu ka bude facebook account wanda ba suna a jiki.

Ku cigaba da kasancewa da wannan shafi mai albarka.

Sunday

INEC : YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .

YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .


Zaben 2019, Gen Buhari, Dr Atiku


Yau saura kwanaki 2 kacal wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na kowane mai son yin za6e a 2019 ya garzaya maza6ar da yayi rajista domin tabbatar da sunan sa. Tare kuma da kai korafin sa a cibiyar mazabar sa (ward center) idan bai ga sunan sa ba, ko kuma akwai matsala a sunan na sa.

GA DAMA TA SAMU !

Idan ba ka da iko na zuwa mazabar ka domin duba sunan ka, to za ka iya amfani da wayar ka domin duba sunan ka.

Ga yadda abin ya ke :

HANYA TA FARKO

1 - bude manhajar ka ta Opera ko UC Browser sai ka yi bincike ta Google a wannan adireshin :
Voters.inecnigeria.org

Akwai bayanan katin zaben ka da za a nemi ka cike a wannan shafi :

i- sunan jihar ka,
ii- sunan mahaifin ka,
iii- sunan ka,
iv- kwanan watan haihuwar ka (date of birth).

MISALI :
i- KANO
ii- MUHAMMAD
iii- IBRAHIM
iv- 01-10-2000.

KO KUMA :

(i) sunan jihar ka,
(ii) sunan ka (First name),
(iii) lambobi biyar NA KARSHEN VIN ( Voter's Identification Number ) da ke a cikin katin zaben ka, (kana kuma iya sa su gabaki daya).
Sannan ka aika.

MISALI :
i - KANO
ii - IBRAHIM
iii- 01234.

HANYA TA BIYU

2 - ka aika da sunan # Jihar ka, da # Sunan ka, da kuma lambobi 5 na kashe a VIN naka dake a cikin katin zaben ka zuwa ga WANNAN LAMBA :
20120, ko kuma: 08171646879.

MISALI :
KANO
IBRAHIM
01234
zuwa ga 20120, ko 08171646879.

Allah Ya bada sa'a.

A TUNA CEWA KATIN ZABEN KA SHI NE MAKAMIN KA WAJEN FATATTAKAR DUK SHUGABAN BA YA KYAUTATA MAKA, TARE DA ZABEN WANDA KAKE SO YA SHUGABANCE KA.

Allah Ya yi mana zabi mafi alheri. Ameen.

Saturday

Yadda zaku samu Airtel Recharge card Plus 1GB Data *479#

A gaskiya, na buga lambar kuma na samu sako [sms message] daga Airtel cewa ina da kyautar 1GB Data, kuma yana buƙata in sake cajin wasu adadin don buɗe 250MB na mako.

                     Airtel Recharge card Plus 1GB Data *479#

Maganar Gaskiya, bayanin 1GB ba kyauta ba ne. Wasu daga cikcin mutanen mu suna kasa karantawa da kuma fahimtar sakon da aka aika musu  Ta hanyar SMS gare su. amma sai su dinga baza bayanai ba daidai ba. Wannan shine dalilin da ya sa muka rubuta wannan post.

kamfanin Airtel Nigeria subyi amfani da shafinsu na yanar gizo don sanar da tsarin na Airtel Recharge Plus * 479 #. A cikin wannan sakon, zan yi bayanin yadda wannan tsarin yake aiki.


Yadda za a Saita Airtel Recharge Plus 1GB Data a layin wayarka na airtel



Airtel Recharge Plus shi ne sabon tsarin Airtel wanda yake ba ka 250MB kowane mako idan ka sake cajin adadin da ka gani a saƙon da aka aika maka bayan ka danna * 479 #. 



 Airtel Recharge card Plus 1GB Data *479#

zaku  dinga samu 250MB a kowane mako, Suna nufin kenen 1GB a wata. Ba za ku iya amfani da wannan 1GB a haka ba, dole ne sai kun yi cajin kudi a layin ku. Bayan kunyi
chajin kudin ne zasu baku damar amfani da wannan Data 1GB , Wanda zaku samu 250MB a duk sati [mako].



Domin bude wannan free 1GB data,sai kayi chajin kudi dai-dai da adadin da kuka gani a saƙon da Airtel suka aika muku ta hanyar SMS , bayan danna *479# don buɗe Wannan 250MB a duk mako.

Thursday

Bidiyo : Wata mata ta kashe mijinta ta yi yunkurin kone gawarsa.

Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta  ya yada labarin wata mata da ta kashe mijinta sannan ta saka wa gawarsa wuta bayan sun yi wani kazamin fada.
na Facebook

A cewar wanda ya yada labarin, lamarin ya faru ne a jihar Bayelsa, sannan ya kara da cewa lamarin ya jawo hankalin makwabtan ma'auratan wadanda suka kira 'yan sanda. Ya kara da cewa, jami'an 'yan sanda sun zo sun dauki gawar mijin sannan sun tafi da matar.

Ko a kwanakin baya wata Mata ta yi yunkurin Kashe Mijinta Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Ciki Saboda Zai Yi Mata Kishiya Ana zargin wata mata mai suna Amina Banaga Maru dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara da niyar hallaka mijinta ta hanyar soka masa wuka a ciki har sau uku.

Lamarin wanda ya auku a RANAR Litinin, 24 ga watan Yuni, bincike ya nuna cewa matar ta yi niyar halaka mijin nata ne saboda tsantsar kishi. Bayanan da muka samu sun tabbatar mana da cewa ana zargin Amina ta yi wa mijin nata wannan danyen aikin ne saboda niyyar da yake da ita na yi mata kishiya.

GA BIDIYON NAN KASA


Wednesday

Yadda mutanen Najeriya za su ba Duniya mamaki – Cewar Osinbajo

Rahotanni sun zo mana cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa irin kokarin da mutanen kasar nan su ke yi a fannin fasaha, ya na iya ci da kasar gaba. Farfesa Yemi Osinbajo ya ke cewa irin kwazon ‘Yan Najeriya ya na iya zama sanadiyyar kawowa kasar mafita a kan matsalolin fasaha na zamani da za su sa Najeriya ta rikide a sahun Duniya. 

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wani zama da wasu kwararru a kan harkokin kasar waje da masu zuba hannun jari a Najeriya a Birnin New York na Amurka. Babban hadimin mataimakin shugaban kasar watau Laolu Akande ya ke cewa, Osinbajo ya bayyana wannan ne a lokacin da a ka jefe sa da wasu tambayoyi kan rikicin fasahar Duniya.

Osinbajo ya ce: “Ba mu son wani rikici a halin yanzu. Mu na maraba da duk wani kamfani da zai zo kasuwanci Najeriya. Huawei su na Najeriya yanzu haka tare da wasu manyan kamfanoni.” 

KU KARANTA: Gwamnan Yobe zai aika ‘Dalibai zuwa karatu a kasar waje

 “Ba mu kai ga yanke shawara a game da sha’anin fasahar 5G ba. Idan a na maganar fasaha, sai mu tambaya ta ya kasar Sin su ka kai ga haka? Ta ya sauran jama’a su ka yi nisa? Mu ma za mu kai ga haka da kan mu.” 

Mataimakin shugaban kasar ya cigaba da cewa gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da baiwar da Ubangiji ya yi wa Matasan Najeriya wajen cin ma burin kasar.

Wannan zai sa kasar ta yi zarra a ban kasa. “Mu na da kasuwar wayar salula na sama da mutane miliyan 174 a Duniya. Najeriya na cikin manyan kasuwannin salula 10 a ban kasa.” Inji Osinbajo.

 Ya cigaba da cewa: “A Duniya, mu ne na 2 a Duniya wajen kasuwanci ta yanar guzo, bugu-da-kari akwai ‘yan Najeriya miliyan 17 da ke amfani da Facebook.
“Kamfanin Microsoft sun yi alkawarin kafa cibiya ta Dala miliyan 100 a Najeriya domin Nahiyar Afrika.” kamar yadda Laolu Akande ya bayyana a jawabin na sa.

SOURCE LEGIT.NG 

Tuesday

Ba za'a dauki lokaci mai tsayi wajen bayyana sunayen minstoci ba : shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana a game da shirin kafa gwamnatinsa a Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan kusan wata guda da shugaban kasar ya sake darewa kan karagar mulki.

Shugaba Buhari ya yi wannan magana ne ta bakin babban Hadiminsa, Femi Adesina, wanda ya ce a wannan karo, shugaban kasar ba zai dauki dogon lokaci wajen fitar da sunayen Ministocinsa ba.

Femi Adesina ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya yi wata doguwar hira da Mujallar Interview Magazine. Mista Adesina ya yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin dinnan, 24 ga Watan Yuni, 2019. A 2015, shugaban kasar ya dauki kusan rabin shekara ba tare da ya kafa gwamnati ba.

Wannan ya jawo jama’a su ka fara kiransa ‘Baba Go Slow’ watau da Hausa "Uban Masu nawa a Najeriya!"

DUBA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Sha biyu 12 - AREWA24 

Da a ka tambayi Adesina game da lokacin da za a nada manyan mukarrabai a gwamnatin Buhari, sai ya ce jama’a ba za su kara kwana guda na lokacin da bai zama dole ba wajen jiran Ministoci. Mista Adesina ya ce: “Shi kan sa shugaban kasa ya fada da bakinsa cewa wannan karo ba za a jima wajen kafa gwamnati kamar yadda a ka yi a 2015 ba, dalili kuwa saboda yanayin ba daya ba ne.”

A wancan lokaci a wa’adin farko, fadar shugaban kasar ta kowa da cewa an samu bacin lokaci wajen mikawa gwamnati mai zuwa wasu takardu wanda hakan ya yi sanadiyyar dadewar da a ka yi. Idan ku na biye da mu, ku na da labari cewa har yanzu babu wadanda shugaban kasa ya nada face Akanta Janar na kasa da kuma shugaban kamfanin NNPC tun da ya zarce a kan mulki a Watan Mayu.